Buhari bai nada jarumi Nura Hussain a matsayin kwamishinan hukumar aikin hajji ba

Buhari bai nada jarumi Nura Hussain a matsayin kwamishinan hukumar aikin hajji ba

- A makon da ya gabata ne wasu kafafen yada labarai suka dinga ruwaito cewa shugaba Buhari Ya nada Nura Hussain a kwamitin aikin Hajji na kasa

- A binciken da gidan rediyon Dabo FM yayi, ya gano cewa babu tushe balle makama a wannan zancen da ke yawo

- Nura Hassan Yakasai ne a cikin takardar, babban ma'aikaci ne a bankin UBA da ke jihar Kano

A satin da ya gabata ne wasu kafafen yada labarai na Hausa suka dinga wallafa cewa, Shugaba Buhari ya ba wa jarumi Nura Hussaini mukami a kwamitin hukumar aikin Hajji ta kasa.

Sai dai bayan bincike da Dabo FM ta gudanar, ta tabbatar da cewa babu tushe balle makama a wannan zancen. Hasalima, sunan Nura Hassan Yakasai ne a dauke a takardar.

Dabo FM ta tabbatar da cewa, Nura Hassan Yakasai da shugaba Buhari ya ba wa mukamin kwamishinan hukumar aikin Hajjin, babban ma'aikaci ne a bankin UBA dake jihar Kano.

DUBA WANNAN: Wani bakatsine ya sauya sunansa daga Buhari zuwa Sulaiman

Jarumi Nura Hussaini kuwa, ya samu tattaunawa da gidan talabijin na Dimokaradiyya. Ya shaida cewa: "Ba a bani mukamin komai ba. Nayi matukar mamaki a lokacin da naji wannan labarin. Hankalina ya kasa dauka, kuma ban yadda da cewa ni ne ba.

"Sunanmu dai yazo iri daya ne da wanda aka ba wa mukamin."

Jarumin ya ce, duk da kasancewar ba shi aka ba wa mukamin ba, yana mika godiyarsa bisa ga murna da Alla-sam barka da jama'a suka dinga masa. Ya ji dadin addu'o'in da ya samu daga al'umma tare da fatan alheri. Ya kara da cewa, dama bai saka a ka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel