Obasanjo ya kai wa El-Rufa'i ziyarar bazata a Kaduna

Obasanjo ya kai wa El-Rufa'i ziyarar bazata a Kaduna

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kai wa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ziyarar bazata a ranar Laraba.

Wasu jami'an gwamnatin jihar Kaduna sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun yi mamakin ziyarar tsohon shugaban kasar saboda basu da masaniyar zuwansa, kawai ganisa suka yi.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, ce ta karbi tsohon shugaban kasar yayin da ya isa fadar gwamnatin jihar Kaduna (Sir Kashim Ibrahim House).

Obasanjo ya kai wa El-Rufa'i ziyarar bazata a Kaduna

Obasanjo da El-Rufa'i
Source: Twitter

Ko a cikin makon jiya sai da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yar da zango a gidan gwamnatin jihar Kaduna a hanyarsa ta zuwa Abuja bayan ya kammala wata ziyara a mahaifarsa, garin Daura.

DUBA WANNAN: Majalisar sarakuna: Gwamnatin Kano ta yi martani a kan hukucin kotu

El-Rufa'i ya kasance daya daga cikin ministoci masu karfi da fada 'a ji' a gwamnatin Obasanjo a karkashin jam'iyyar PDP.

Sai dai, ana ganin dangantaka tsakanin 'yan siyasar biyu ta samu rauni bayan sun bar gwamnati, musamman saboda canjin shekar El-Rufa'i zuwa jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel