San barka: Hadiza Gabon ta taimakawa samari masu tuyar kosai da jari

San barka: Hadiza Gabon ta taimakawa samari masu tuyar kosai da jari

- Wani bidiyon wasu samari masu tuyar kosai a bakin titi ya karade kafafen sada zumuntar zamani

- Hakan ne kuwa yasa Jaruma Hadiza gabon ta lalubo samarin ta hannun Darakta Hassan Giggs

- Ta ba samarin wasu makuden kudade domin su samu su kara jari, ta jinjinawa rashin girman kansu

A ranar 4 ga watan Disamba 2019 newani bidiyo dauke da wasu samari masu tuyar kosai ya mamaye shafukan sada zumunta, cike da ban mamaki da al’ajabi ganin samari masu tuyar kosai a wannan lokaci da muke ciki na girman kai da son abun duniya.

Bidiyon dai ya samo asali ne daga daraktan fina-finan hausa, Hassan Giggs inda ya saka a shafin sa na Instagram. Yana ba wa yaran shawara tare da basu karfin guiwa a kan sana’ar da suke yi.

San barka: Hadiza Gabon ta taimakawa samari masu tuyar kosai da jari
San barka: Hadiza Gabon ta taimakawa samari masu tuyar kosai da jari
Asali: Facebook

Saurayi mai suna Salim Ahmad Ishaq tare da abokinshi Ahmad Yakubu, mazaunan takuntawa ne a jihar Kano. Samarin sun bayyana yadda wannan sana’ar ta suyar kosai ta rufa musu asiri. Sun yi gida da wannan sana’ar. Suna yin koko, kosai, fanke da awara.

Sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta daga mutane. Wasu mutanen kan yi musu dariya tare da musu ba’a sakamakon ganinsu a matsayin maza amma suna wannan sana’ar. A kan dangantasu da ‘yan daudu duk da ba hakan suke ba.

KU KARANTA: Babbar magana: Hotunan yadda aka daura auren wata mata da kafet din dakinta

Ganin wannan bidiyon ne yasa Jaruma Hadiza Gabon ta bukaci Daraktan da ya nemo mata wadannan samarin. Bai kuwa yi kasa a guiwa ba ya nemosu.

Bayan nemosu din ne, jarumar ta bada wasu makuden kudade don a ba wa samarin don kara karfafa musu guiwa. Hakan ya jefa samarin cikin halin farinciki da annashuwa. Don har kukan dadi suka yi a kan wannan kyautar. Sun bayyana cewa, daga yau ta zamo mahaifiyarsu ta biyo. Sun yi ma jarumar fatan alkhairi.

Sai dai Darakta Hassan Giggs ya ce ba da yawun jarumar ya sanarwa duniya wannan taimakon da ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng