Jami'ar Bayero ta Kano ta kara kudin makaranta, ta bayyana dalilanta
Jami’ar Bayero da ke Kano, ta tabbatar da karin kudin makaranta da na hayar dakunan kwanan dalibai da ke cikin makarantar. Ta ce karin ya biyo bayan hauhawar kayayyaki a kasar nan.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, jami’ar ta sanar da hakan ne a mujallarta da ke fita duk mako. Ta sanar da karin kudin makarantar da na dakunan kwanan dalibai, lamarin da ya jawo maganganu da guna-gunin dalibai da jama’ar gari.
Kamar yadda mataimakin shugaban jami’ar, Haruna Wakili, ya sanar da manema labarai a ranar Litinin, yace wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar da bangarori da dama na makarantar suka bayyana na karin kudin makarantar.
Kamar yadda ya ce, hukumar jami’ar ta kara kudin dakunan kwanan daliban ne don ta mayar dashi dai-dai da yadda daliban Najeriya da kasahen ketare ke biya.
DUBA WANNAN: Kotu ta yanke wa matar da ta kashe kishiyarta da 'ya'yan ta 7 hukuncin kisa
Ya bayyana cewa, daliban Najeriya masu digiri na biyu ko na uku na biyan N60,000 ne na dakin kwana, inda daliban ketare ke biyan N80,000. A don haka ne hukumar jami’ar ta kara dubawa don mayar da kudin duk daya.
Wakili ya bayyana cewa, jami’ar ta kara N200 ne kacal a kan kudin makaranta, sauran karin kuwa na hukumar gudanarwar jami’ar ne.
“A kan karin kudin dakunan kuwa, an karawa wadanda suke zama ne a dakunan makaranta. Bari in sanar daku, dakunan makarantar mu na iya daukar kashi 18 ne kacal na dalibanmu,” Wakili ya sanar.
Wakili ya kara jaddada cewa, karin ba kowanne dalibi ya shafa ba, amma kafafen yada labarai suna ta zuzuta lamarin.
Wakili ya tabbatar da cewa, hukumar jami'ar bata bukaci jin ta bakin kungiyar daliban jami’ar ba, ganin cewa akwai matukar bukatar kari kudin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng