Tsofaffin gwamnoni 9 da EFCC ke zarginsu da satar kudi, amma har yanzu shiru kake ji

Tsofaffin gwamnoni 9 da EFCC ke zarginsu da satar kudi, amma har yanzu shiru kake ji

Tun bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke a kan tsohon gwamnan jahar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu wanda ake zarginsa da satar fiye da naira biliyan 7, inda ta daure shi shekaru 12 a kurkuku bayan shekara 12 ana shari’a, yan Najeriya da dama sun bayyana mabanbanta ra’ayi game da hukuncin.

A nan ma jaridar Punch ta ruwaito akwai wasu tsofaffin gwamnoni guda 9 wanda hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, take zarginsu da satar kudi a zamaninsau, amma har yanzu shiru kake ji kamar mushiriki ya ci shirwa ya sha ruwa.

KU KARANTA: Osinbajo ya tafi kasar Dubai domin ganawa da yariman kasar mai jiran gado

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wadannan tsofaffin gwamnoni sun hada da Sanata Ali Modu Sheriff, Rabiu Musa Kwankwaso, Aliyu Magatakarda Wammako, Danjuma Goje, Theodore Orji na Abia, Timipre Sylva na Bayelsa, Godswill Akpabio na Akwa Ibom, Peter Odili na Riversda Sullivan Chime na jahar Enugu.

Ga takaitaccen jawabi a kan tsofaffin gwamnonin jahohin yankin Arewa dake cikin jerin gwamnonin:

Ali Modu Sheriff:

Hukumar EFCC na zargin tsohon gwamnan jahar Borno, Ali Modu Sheriff da barnatar da makudan kudi naira biliyan 300 a zamanin daya mulki jahar daga shekarar 2003 zuwa 2011, inda har ta kama shi a shekarar 2015, amma kuma ya samu beli a gaban kotu.

Ko a watan Feburairun shekarar 2016 sai da EFCC tace tana cigaba da gudanar da bincike a kan Modu, amma daga nan ba’a sake jin duriyar shari’ar Sheriff ba, wanda suruki ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rabiu Kwankwaso:

Tun bayan saukarsa daga mukamin gwamnan jahar Kano a shekarar 2015 ne hukumar EFCC ta bayyana cewa ta fara binciken Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a kan wasu kudi naira biliyan 3.08 da tace ya wawura daga kananan hukumomin jahar 44.

EFCC ta zargi Kwankwaso da tilasta ma kowacce karamar hukumar jahar Kano da bashi kyautar naira miliyan 70 wanda ya yi amfani dasu wajen gudanar da yakin neman zabensa. Amma shima har yanzu babu zance babu amo.

Aliyu Wammako:

Wammako ya mulki jahar Sakkwato daga shekarar 2007 zuwa 2015 bayan saukan Attahiru Bafarawa, sai dai tun a shekarar 2015 hukumar EFCC take bincikensa a kan zargin satar naira biliyan 15.

Sai dai shi ma kamar sauran takwarorinsa, har yanzu EFCC bata gurfanar da shi gaban kotu ba, wanda hakan ke alanta kamar batunsa ya sha ruwa kenan.

Danjuma Goje:

Jim kadan bayan saukarsa daga kujerar gwamnan jahar Gombe a shekarar 2011, Danjuma Goje ya fada hannun hukumar EFCC, inda take zarginsa da satar naira biliyan 5, an yi ta yin wannan sharia har 2019.

Majiyarmu ta ruwaito an kashe sama da naira miliyan 100 a shari’ar, kuma shaida 25 sun bayyana a gaban kotu a yayin wannan shari’a, ko a ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2019 sai da babbar kotun tarayya dake Jos ta tabbatar da cewa Goje fa yana da tambayoyin da zai amsa, amma daga karshe gwamnati ta janye karar da take masa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng