Goje ya yi murabus daga siyasar tsaya wa takara

Goje ya yi murabus daga siyasar tsaya wa takara

Lamarin yazo cike da ban mamaki, Tsohon Gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar jihar Gombe ta tsakiya, Muhammad Danjuma Goje ya sanar da murabus dinsa a siyasar tsaya wa takara. Ya yi hakan ne don ba wa sauran 'yan siyasar jihar masu tasowa damar nuna bajintarsu.

Sanatan ya sanar da hakan ne a yayin taron mambobin APC da 'yan siyasa magoya bayansa a filin wasa na Pantami a ranar Lahadi. Amma kuma ya jaddada cewa, hakan ba yana nufin zai bar siyasa kwata-kwata bane. Zai ba na baya ne dama su nuna bajintarsu. "Da izinin Ubangiji idan ina raye, zan fito don kamfen a 2023."

Kamar yadda yace, akwai 'yan siyasar da ke ganin kamar ya dishe musu tauraruwarsu, "Lokaci ya yi da zan bar wa na baya inda na tsare a siyasar takara. Daga yanzu, fili a bude yake ga duk mai bukatar neman kujerar sanatan da nake kai a yanzu idan 2023 tayi".

DUBA WANNAN: Arewa: Jihohi biyar da suka fi talauci a Najeriya da dalilin talaucinsu

A matsayinsa na madubin dubawa a siyasar jihar, zai cigaba da goyon bayan Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da kuma jam'iyyar APC a jihar. Ya kara da alkawarin biyayya da goyon baya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawal da kuam shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

A yayin alkawarin cigaba da tabbatar da shugabanci nagari a kowanne mataki, Sanata Goje ya ce, ya yanke wannan hukuncin ne ba don fusatawa ko harzuka magoya bayansa ba ko jama'ar jihar. Ya mika godiyarsa garesu da suka bashi damar hidimta musu a mataki daban-daban na karamar hukumar, jiha da kuma tarayya.

A take kuma ya bada kyautar naira miliyan 19 ga shuwagabanninin jam'iyyar tun daga matakin gunduma har zuwa jihar. Ya kara da bada motoci, a daidaita sahu da babura kyauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel