Gumi: Ya kamata tsofaffin ‘Yan siyasa su tafi su ba yara wuri a zaben 2023

Gumi: Ya kamata tsofaffin ‘Yan siyasa su tafi su ba yara wuri a zaben 2023

A cewar fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, Mutanen Arewa sun koyi hankali a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Malamin ya bayyana mutanen Najeriya da masu ‘dan-karen son rai, sannan kuma marasa daukar darasi. Shehin Malamin ya yi magana ne game da abin da ya shafi siyasar 2023.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ke cewa abin da ake bukata yanzu shi ne kasar nan ta zauna daidai, ba a buge da siyasar bangaranci ba, Malamin ya ce hakan ba mafita ba ne.

Gumi ya kara da cewa abin da Najeriya ta ke bukata shi ne mutane masu basira da tunani, wanda a cewarsa bai da alaka da Yankin da mutum ya fito na Kudu ko Arewacin kasar.

Malamin ya ce sha’anin mulki bai da alaka da ko mutum ya fito ne daga Yankin Kudu ko Gabas ko Yamma. Gumi ya tunawa jama’a yadda Umar Yar’Adua ne ya fara aikin jirgin kasa.

KU KARANTA: Malami ya ba Ganduje shawara a kan nada sababbin Sarakuna

“Arewa ta koyi hankalinta. Yanzu Arewa ta fi kowa shan wahala a karkashin Buhari. Jonathan ya gina makarantun Almajirai 150 a Arewa, Jami’o’i 9 a Arewa. Ya na ta faman aiki.”

Da Fakihin ya ke zayyano halin da ake so shugaba ya kasance da shi, sai ya lissafo, basira, wanda bai da nufin ramuwar gayya, mai afuwa da gyara mutane ba mai daure su ba.

Har ila yau, a hirar da aka yi da Bajimin Malamin, ya kara da cewa bai kamata a samu shugaban da ya ke tunanin yadda zai rika damke mutane, a maimakon ya rika yi masu gyara ba.

A cewarsa an ga cigaba daga 1999 i yau, amma ta fuskar mulki, an ci baya. “Ya kamata abubuwa su inganta dalilin samuwar kimiyya da fasaha, wanda ya kusanta jama’a da juna.”

“Gwamnati ta na ci baya ne saboda an rasa mutanen da su ka dace, a inda ya dace, a lokacin da ya dace. Halin da ake ciki a Najeriya ya dada tabarbarewa ne matuka a yanzu.” Inji Gumi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel