Jaruma Rahama Sadau ta cika shekaru 26 a duniya

Jaruma Rahama Sadau ta cika shekaru 26 a duniya

Sananniyar jarumar Nollywood da Kannywoood, Rahama Sadau ta cika shekaru 26 a ranar Asabar da ta gabata. Ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram a ranar.

Abun farinciki da jindadi, an haifeni a irin wannan ranar a shekarar 1993. Ina taya kaina farincikin cika shekaru 26 a duniya. Ina wa kaina fatan zaman lafiya, farin ciki da annashuwa. Ina fatan shawo kan duk wasu wahalhalu na rayuwa cikin sauki, ina fatan kowacce rana ta cika da farinciki da murna, Amin ya Allah!!!”

“Ina wa kaina fatan shekaru masu yawa su zo cikin koshin lafiya. Kada a wuce ba tare da an yi min addu’a ba." Ta walllafa a shafinta na Instagram.

An haifa jaruma Rahama Sadau ne a ranar 7 ga watan Disamba, 1993. Ta kuwa yi suna ne a masana’antar bayan da kungiyar tace fina-finai ta dakatar da jarumar. An zargeta ne da rashin natsuwa ko kama kai da ya watsu ta wata waka da ta bayyana a bidiyonta, tare da wani mawaki a shekaru uku da suka gabata.

DUBA WANNAN: A matse nake in yi aure - Jaruma Saima Muhammad

Idan zamu tuna, MOPPAN ta dakatar da jarumar ne a ranar 2 ga watan OKtoba, 2016 bayan da ta bayyana a wani faifan wakar hausa tare da mawaki ClassiQ.

Wasu daga cikin magoya bayan jarumar sunce, tauraruwarta ta kara haskawa ne bayan da aka dakatar da ita din. Hakazalika, duniya ta kara sanin jarumar.

Kwanaki kadan bayan an dakatar da ita, ta samu goron gayyata daga babban mawakin duniya na kasar Amurka mai suna Akon. An gano cewa, ta bayyana a wani faifan bidiyon wakarsa a lokacin da ta kai ziyarar. Bayan dawowar tane ta bayyana a wani fim din kudancin kasar nan mai suna “Tatoo”.

Wannan ne kuwa ya zama mabudinta na fara shiga fina-finan kudancin kasar nan. Daga cikin fina-finanta na Nollywood akwai, Up North, MTV Shuga Naija da sauransu.

A farkon shekarar nan ne Rahama ta kammala digirinta daga wata shahararriyar jami’a da ke kasar Cyprus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng