Rikici da Mai dakin Tinubu, fada da hukuma da sauran rikicin Melaye

Rikici da Mai dakin Tinubu, fada da hukuma da sauran rikicin Melaye

Za a dade ba a manta da Sanata Dino Melaye a Najeriya ba, saboda irin hatsaniya iri-iri da ya shiga a lokacin da ya ke gwagwarmaya har zuwa tafiyar sa majalisar wakilai da dattawan kasar.

Sanatan da yanzu ya rasa kujerarsa a hannun APC bayan an yi mai-man zabe. Dino Melaye ya sha alwashin karbe kujerarsa a kotu. Kafin nan Daily Trust ta kawo wasu abubuwan da ya yi a baya.

1. Goyon bayan Bukola Saraki

Za a rika tuna Dino Melaye a matsayin ‘Dan a-mutun Bukola Saraki a majalisa. Goyon bayan da ya ba tsohon shugaban majalisar dattawan kasar ya hada shi fada da masu rike da madafan iko.

2. Rikici da Sanata Remi Tinubu

Dino Melaye ya yi rikici da Mai dakin Jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu, watau Oluremi Tinubu, inda ya kira ta abn da bai dace da Matar aure ba. A cewarsa, Sanatar ce ta soma kiransa kare.

3. Takaddama da Dakarun DSS

‘Dan majalisar ya samu kansa a cikin halin rikici da jami’an DSS a wani lokaci da aka dauke shi daga asibitin cikin Gari zuwa asibitin DSS, a nan Sanatan ya yi rashe-rashe a kasa ya jawo surutu.

4. Wasan kwaikwayo

Idan ba ku manta ba, Dino Melaye ya fito a cikin wani shirin wasan kwaikwayo na Nollywood. A na sa ran cewa nan gaba kadan wannan fim zai fito kasuwa bayan Sanatan ya rasa kujerar ta sa.

5. Hawa manyan motoci

Sanata Dino Melaye ya na da sha’awar lumbutsa-lumbutsan motoci masu numfashi. Akwai wani bidiyo da ya yi ta yawo wanda a ka ga Hon. Gujadi Kazaure ya gigice da ya ga motocin Sanatan.

6. Fitowa daga cikin motar ‘Yan Sanda

A yunkurin tafiya da Dino Melaye zuwa ofishin ‘Yan sanda a Garin Lokoja, inda ake zarginsa da laifin kisa, Melaye ya yi tsalle ya fado daga cikin mota yayin da ta ke gudu, dole ya kare a asibiti.

7. ‘Dan-karen kwalliya

Za a rika tuna tsohon Sanatan na Kogi da irin tufafin kwalliyar da ya saba sanyawa. Jaridar ta ce don haka ne ma wasu Abokan aikinsa ke kiransa “Babalawo” ko “Kabiyesi” idan ya shigo zaure.

8. Tallar gyada

A baya an taba ganin hotuna da bidiyon ‘dan majalisar dattawan ya na saida gyada. Sanatan PDP ya daura farantin gyadar ne a saman kansa, ya na yawo ya na talla a cikin Gari a bainar jama’a.

9. Mawakin Sanata

Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, Melaye ya saba rangada wakoki. Sanatan ya kan wallafa bidiyon wadannan wake-wake na sa a dandalin sada zumunta. Za a dade ba a manta da wannan ba.

10. Tirka-tirkar shaidar karatu

A farkon 2017, aka fara yada wutan zargin cewa Dino Melaye bai kammala karatu daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da sauran makarantun da ya ke ikirari ba. A karshe an karyata wannan.

11. Yunkurin kiranye

Melaye ya gamu da barazanar kiranye daga majalisa a 2017. Sai dai wannan yunkuri bai kai ko ina ba, bayan INEC ta tabbatar da cewa kashi 5% na mutanen mazabarsa kadai su ka sa-hannu.

12. Dambe a Majalisa

Honarabul Dino Melaye ya na cikin wadanda aka taba dakatarwa daga majalisar wakilai a 2010. An hukunta ‘Dan majalisar a lokacin ne bayan ya shiga cikin damben da aka tafka a majalisar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng