Jaruma Rahama Sadau za ta fara abincin siyarwa

Jaruma Rahama Sadau za ta fara abincin siyarwa

Fitacciyar jarumar Kannywood da ke jan zarenta a wannan karnin, Rahama Sadau, ta bada sanarwar bude katafaren gidan abincin siyarwa mai suna Sadau Home, wanda zata bude a garin Kaduna kwanaki kadan daga yanzu.

Jarumar ta wallafa hotonta sanye da kaya irin na kuku da kuma hoton abinci a gefe inda ta hada da sanarwar bude katafaren gidan abincin. Wajen na hade da gidan kwalliyar ta da sauransu wadanda ta ke kira da Sadau Home. Ta bayyana abubuwan da za a iya samu a Sadau Home sun hada da Abinci kala-kala, gyaran jiki na mata, wurin kwaliiya, wurin gyaran gashi, wurin shan shisha, wurin gasa nama da sauransu.

DUBA WANNAN: Mu masu gyaran tarbiya ne - Teema Makamashi

Koda yake ba tun yau Rahama Sadau ta fara wannan shiri ba, domin an dade ana ganin yar uwarta Zee Sadau tana wallafa hotunan kala-kalar abinci na ‘yan gayu a shafinta na Instagram. Hotunan suna dauke da tambarin Sadau Kitchen a jiki, wanda tun a lokacin aka fara tunanin wani abu makamancin hakan.

Tabbas Rahama Sadau sai dai ace sambarka, domin kuwa likkafa kullum gaba take ci. Tunda fari dai jarumar bayan haskawar tauraruwarta, ta fara ne da bude gidan kwalliya inda daga bisani jarumar ta bude kamfanin sarrafa jambakin mata. Yanzu kuma zata bude katafaren gidan cin abinci baya ga kamfanin shirya fina-finai da ta mallaka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel