Aikin da Buhari yayi a Najeriya yafi na shekaru 16 da Obasanjo, 'Yar Adu'a da Jonathan suka yi akan mulki - Sagay

Aikin da Buhari yayi a Najeriya yafi na shekaru 16 da Obasanjo, 'Yar Adu'a da Jonathan suka yi akan mulki - Sagay

- Shugaban kwamitin PACAC, ya caccaki masu kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yunkurin karbo bashi

- Ya ce jahilci ne da munafunci da gangan yasa suke sukar batun karbar bashin don yin aiyukan raya kasa

- Sagay yace, a aiyukan da Buhari ya aiwatar, ba za a hadashi da Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan ba saboda ya yi musu fintinkau

Shugaban kwamitin PACAC ya kwatanta wadanda ke kalubalantar Buhari da jahilai kuma munafukan da suka kasa banbance bashi da yawan manyan aiyuka.

A yayin tattaunawa da jaridar Daily Independent, Sagay ya ce: "Zan iya cewa ya yi aiyuka manya fiye da Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan.

"Ba a iska ake samun hakan ba, da kudi ake samun gudanar da hakan.

"Ina tunanin cewa, mutanen da ke kalubalantar bukatar bashin Buhari sun jahilci abun ne, saboda bashin ba aibu gareshi ba. Abinda aka yi da bashin ne abun dubawa."

KU KARANTA: Wa'iyazubillah: An kama dan sanda a lokacin da yake tsakiyar lalata da gawa

Idan ba mu manta ba, an bayyana yadda Buhari ya kara mika bukatar karbo bashi don aiwatar da wasu manyan aiyuka a Najeriya ga sabuwar majalisar dattijai. Wannan bukatar kuwa ta ki karbuwa ne a waccan majalisar da ta gabata. Kara mikata gaban wannan sabuwar majalisar kuwa ta jawo cece-kuce inda wasu je ganin rashin amfanin karbo bashin, ya fi amfaninshi yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel