Ana kutun-kutun na sauke Seyi Makinde daga mulki a Kotun koli – PDP
Jam’iyyar PDP ta reshen Kudu maso Yammacin Najeriya ta zargi fadar shugaban kasa da yunkurin amfani da kotun koli ta ruguza nasarar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya samu.
Babbar jam’iyyar hamayyar a Najeriya, ta ce akwai shirin da ake yi na karbe mulki daga hannun Seyi Makinde wanda ya yi nasara a cikin kananan hukumomi 28, yayin da APC ta yi nasara a 5.
Jam’iyyar ta yi wannan bayani ne a wani jawabi da ta fitar a karshen zaman da ‘Ya ‘yanta su ka yi a Garin Abeokuta da ke jihar Ogun. Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton wannan zama da aka yi.
Daga cikin wadanda su ka halarci taron akwai manyan jiga-jigan jam’iyyar irinsu; Yemi Akinwonmi; Sanata Ibrahim Kazaure, Dr. Eddy Olafeso, Dr. Doyin Okupe, da Femi Fani-Kayode.
Sauran wadanda aka yi zaman da su sun hada da manyan PDP da kusoshi gwamnatin Oyo: Bisi Ilaka da Ladi Adebutu da sauransu. Jagororin sun kuma soki hukuncin kotun daukaka kara.
KU KARANTA: Albashi biyu: Sanatoci da Ministocin da hukuncin kotu ya shafa
A cewar ‘ya ‘yan PDP, hukuncin da kotun daukaka kara ya yi a game da zaben jihar Oyo, shi ne ya zo da kwamacala. A baya an rusa nasarar da PDP ta samu a 2019, amma aka ki tsige gwamnan.
PDP ta ce: “Mu na kara jaddadawa mutane cewa PDP ta doke APC ciki-da-bai a zaben gwamnan jihar Oyo, ta yi nasara a kananan hukumomi 28, yayin da APC kuma ta yi nasara a 5 kacal.”
“Hukuncin da zai yi daidai da abin da mutane su ke so a Oyo shi ne wanda ya ba PDP gaskiya. Hujjojin APC ko da an saurare su a gaban kotun zabe, ba za su iya ruguza sakamakon zaben ba.”
Jam’iyyar adawar ta bukaci a sake duba batun yi wa tsarin zabe garambawul. A karshen jawabinta, ta yi Allah-wadai da yadda jami’an tsaro su ka yi wa APC aiki a zaben Kogi da Bayelsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng