Alaramma da ya amshi naira biliyan 1 don cusa haddar Qur’ani a kan wani ya shiga hannun EFCC

Alaramma da ya amshi naira biliyan 1 don cusa haddar Qur’ani a kan wani ya shiga hannun EFCC

Jami’an hukumar EFCC reshen jahar Kaduna sun kama wani malamin addinin musulunci, da yake ikirarin shi alaramma ne a bangaren haddar Qur’ani mai suna Abdulrashid Imam da laifin damfarar wani mutumi Muhammad Dewu zambar kudi dalan Amurka miliyan 3, kimanin naira biliyan 1.093 kenan.

Legit.ng ta ruwaito EFCC ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke Alaramma ne bayan Dewu ya aika mata da rubutaccen korafi inda ya zargi Alaramma da damfararsa $3,024,000, kimanin N1,093,176,000 kenan a kudin Najeriya.

KU KARANTA: Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya shiga majalisar dattawa

Dewu yace ya baiwa Alaramma wadannan kudade ne saboda Alaramman yace yana da ikon cusa masa haddar Al-Qur’ani izu 60 kacokan a kansu ta hanyar amfani da wasu aljanu da yake amfani dasu, inda shi kuma Dewu masoyin Al-Qur’ani ya yarda.

Dewu, ya cigaba da cewa a kokarinsa na samun wannan garabasa, Alarmma ya bukaci ya kawo wasu abubuwa kamar haka:

- Kwalba 2 na wani turare a kan kudi N70,000

- Kwalba 1 na wani turare a kan kudi N160,000

- N550,000 na wani kwalban turare don maganin ciwon kafa dake damun mahaifiyarsa

- N1,680,000 na kwalabe 60 na turarukan da zasu tashi ayoyin Qur’anin da zasu shige cikin kansa da ikon Aljanu

- N20,000 na wayoyin salula guda 2 da layin waya

- Bokiti 30 na zuma, wanda zasu tabbata ayoyin Qur’anin sun shiga cikin kansa

Baya ga amsan wadannan kudade da kayayyaki, sai Alaramma ya bukaci Dewu ya bashi kudi dala dubu 24, a cikin sati na uku na watan Oktoba, na shekarar 2019, haka zalika ya nemi Dewu ya bashi dala dubu 120 domin ya samar masa da wasu kudade da zasu fado daga sama zuwa cikin dakinsa a cikin akwatuna guda biyu.

A wani labari kuma hukumar EFCC ta samu nasara a gaban wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Legas inda kotun ta yanke ma tsohon gwamnan jahar Abia, kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Orji Uzor Kalu hukuncin daurin shekaru 12 a kurkuku bayan kama shi da laifin satar naira biliyan 7.65.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel