Sharik Tobar: Kyakkyawar budurwar da take shafe wata biyu cur tana bacci ba tare da ta tashi ba

Sharik Tobar: Kyakkyawar budurwar da take shafe wata biyu cur tana bacci ba tare da ta tashi ba

- Budurwar ta yi kwanaki 48 cikin watanni biyu tana sharara bacci, mahaifiyarta ce ke kula da ita wajen ciyarwa a baccin

- Wannan mugun baccin na cigaba da yi mata illa don kuwa ta rasa kwayar halittar da da ke bata damar tunawa da abubuwa

Wata budurwa mai suna Sharik Tobar mai shekaru 17 an gano tana da ciwon yawan bacci. Budurwar ‘yar asalin kasar Kolombiya ce wacce ake wa lakabi da ‘Kyakyawa mai ciwon bacci,’. An saka mata hakan ne bayan da budurwar ta yi baccin wata biyu a jere.

Sharik Tobar tana zaune ne a birnin Acacias da ke kasar Kolmbiya kuma tana dauke da cutar da likitoci ke kira da Kleine-Lebin. Ta kamu da cutar ne tun tana da shekaru biyu a duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa, masu irin wannan cutar su 40 ne kacal a duniya, kuma suna kasancewa cikin yawan bacci ne a rayuwarsu.

Idan Sharik ta fara baccin, tana yin wata biyu a wannan hali. Mahaifiyarta ce ke ciyar da ita abinci mai ruwa-ruwa lokaci zuwa lokaci don lura da lafiyarta a yayin baccin.

“Bayan baccin kwana 48 a watan Yunin bara, ta rasa kwayar halittar da ke bata damar tuna abu a kwakwalwarta. Hakan yasa wata rana Sharik ta tambayi mahaifiyarta ita wacece,” kamar yadda Marleny mahaifiyar Sharik ta bayyana.

KU KARANTA: Tirkashi: Uba ya kashe saurayin 'yarsa ya auri abar shi

A bana kuwa, tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu, Sharik ta yi baccin kwana 22. Mahaifiyarta ta aje aikinta don samun kulawa da ‘yarta maimakon mika Sharik ga hukumomin kasar Kolombiya.

Akwai lokacin da mahaifiyar Sharik ta fara neman taimako saboda yarinyarta ta fara komawa kurma. Hakan yasa shugaban karamar hukumar Acacias ya basu gudunmuwar gida a maimakon gidan hayar da suke ciki.

Shugaban karamar hukumar Orlando Gutierrez, ya bayyana cewa, a halin yanzu suna ci gaba da gina madatsun ruwa a yankin da budurwar take don tanadar wa jama’a wadataccen ruwa.

Mahaifiyar budurwar ta bukaci taimakon masana lafiya a kan cutar Sahrik saboda kada ta rasa wani bangaren na kwakwalwarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel