Babbar magana: Sayar da wiwi a jinina ne, dan haka babu wanda ya isa ya hanani - Wani dilan wiwi ya fadawa hukumar NDLEA

Babbar magana: Sayar da wiwi a jinina ne, dan haka babu wanda ya isa ya hanani - Wani dilan wiwi ya fadawa hukumar NDLEA

- Jami’an hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wani mutum da jakkuna 106 na ganyen wiwi

- Umaru Shehu ya bayyanawa manema labarai cewa ba zai iya dena wannan sana’ar ba saboda a jininshi take

- Ya yi bayanin yadda ya taho da wannan ganyen tun daga jihar Legas kuma yake fatan kaiwa Sokoto amma sai jami’an suka kamashi

Siyar da wiwi a jinina yake- Wannan ne kalaman da suka fito daga bakin wani mutum mai suna Umaru Shehu, wanda jami’an yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi suka cafke. Sun kama Umaru Shehu ne yayin da yake safarar ganyen wiwi zuwa jihar Sokoto.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, an kama mutumin da jakkuna 106 na ganyen wiwi kuma ya bayyanawa manema labarai cewa, da wuya ya bar wannan sana’ar.

An cafke Umaru Shehu ne a babban titin Mokwa na jihar Neja kuma an gano cewa, ya taba zama gidan gyaran hali a kan wannan sana’ar.

A yayin zantawa da manema labarai, wanda ake zargin yace akwai matukar wuya ya iya barin wannan kasuwancin saboda a cikin jininshi yake.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: Wani na hannun daman Jonathan na barazanar kashe wani mutumi

Ya bayyana yadda aka taba garkameshi a gidan yari saboda an kama shi da 64kg na ganyen a shekarun da suka wuce. Ya kara da cewa, ba zai iya barin wannan sana’ar ba. Bai taba tsammanin jami’an tsaro zasu iya bankado ganyen ba, ganin yadda ya boyesu a cikin motar kayan.

“Sana’ar ganyen wiwi a jinina take, akwai matukar wuya in iya denawa. Lokacin da na fara tafiyar nan daga jihar Legas zuwa Sokoto, ban taba tsammanin jami’an tsaro zasu kama ni a Mokwa ba. Wannan ce sa’a ta,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel