Buhari ya nada Zikrullah a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai

Buhari ya nada Zikrullah a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Sheikh Zikrullah Olakunle Hassan a matsayin sabon shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai ta Najeriya biyo bayan karewar wa’adin mulkin tsohon shugaban hukumar, Abdullahi Mukhtar.

Buhari ya sanar da nadin Zikrullah ne cikin wata wasika dake dauke da sunan Zikrullah da sauran sabbin kwamishinonin hukumar daya aika ma majalisar dattawan Najeriya domin ta tantancesu, kamar yadda majalisar ta tabbatar a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Twitter.

KU KARANTA: Abubuwa 5 game da dokar takaita amfani da kafafen sadarwar zamani

Buhari ya nada Zikrullah a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai

Zikrullah Olakunle Hassan
Source: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa Zikrullah ya fito ne daga jahar Osun, yayin da Abdullahi Magaji Hardawa kwamishinan sintiri ya fito daga jahar Bauchi, kwamishinan kudi da tsare tsare,Nura Hussaini Yakasai ya fito daga jahar Kano, sai Sheikh Momoh Suleiman a matsayin kwamishinan watsa labaru da kididdiga wanda ya fito daga jahar Edo.

A cikin wasikar, shugaban kasa ya bayyana ma shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan cewa ya yi wannan sabbin nade nade ne duba da daman da sashi na 3(2) na kundin dokokin hukumar alhazai.

A wani labarin kuma, Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya yi addu’ar Allah Ya saukar da fushinsa a kan duk masu cin mutuncin Al-Qur’ani a jahar Zamfara, sa’annan ya yi kira ga al’ummar jahar Zamfara dasu cigaba da rokon Allah a kan wannan matsala.

Matawalle ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba yayin bude taron gasar Al-Qur’ani mai girma na shekarar 2019 daya gudana a garin Gusau inda yace:

“Wannan addu’an ya zama wajibi saboda masu aikata laifin nan sun tafka mummunan badala wand aka iya janyo mana masifa, don haka haka muyi addu’a kada fushin Allah Ya shafemu.

“A matsayina na gwamna, na kafa kwamitin bincike, kuma duk wanda muka kama da laifi sai ya fuskanci hukunci kamar yadda dokokin shari’ar musulunci suka tanadar, duk girmansa kuwa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel