Jama’a su yi koyi da sassaucin addinin Shugaba Buhari – Osinbajo

Jama’a su yi koyi da sassaucin addinin Shugaba Buhari – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yabawa sassaucin ra’ayin addinin shugaban kasa Muhammadu Buhari, har ta kai ya na kira ga mutane su yi koyi da shugaban.

Mai girma mataimakin shugaban Najeriyar ya yi wannan bayani ne a wajen taron da kungiyar NSCIA ta shirya a babban birnin tarayya Abuja. NSCIA ce babbar majalisar kolin musulunci.

An gudanar da wannan taro ne a Ranar Asabar, 30 ga Watan Nuwamban 2019. Yemi Osinbajo ya ke cewa ra’ayin rikau na addini ya kasance barazana ga kasar nan musamman a lokutan baya.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto, Osinbajo ya bada misalan saukin kan Mai gidan na sa. Sauran manyan kasa irinsu Mai martaba Sarkin Musulmi da Aisha Buhari sun halarci taron.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi magana a kan mutuwar babban ‘Dan kasuwar Kano

“Wasu lokutan idan mu ka hadu a safiyar ranar Lahadi, ya kan tambaye ni ko an kammala ibada a coci ne ko kuma na tsere daga wajen bautar. Irin wannan sassaci mu ke bukata.” Inji Osinbajo.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa: “A kasa irin Najeriya mai tarin Mabiya addinai daban-daban da kuma Kabilu iri-iri, nauyi ne a kan shugabanni su bada misalin abin koyi.”

Farfesa Osinbajo wanda shi kansa Malamin addini ne a cocin nan na RCCG da ya yi fice, ya tabbatar da cewa shugaban kasa Buhari ba mutum ba ne mai ra’ayin rikau mai zafi na addini.

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta ji dadin halartar Yemi Osinbajo wajen taron. Mai dakin shugaban kasar ta ja hankalin shugabanni da su ji tsoron Allah a aikinsu.

A wajen wannan taro da Osinbajo ya samu halarta, Sarkin Musulmi a na sa jawabin ya yi kira ga masu mulki su kawo karshen barace-baracen Almajirai tare da inganta karatun ‘Diya mace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel