To fah: Babu yarinyar da iyayenta za su yadda ta shiga harkar fim da sanin su, ko nima sai da na samu matsala da su kafin na fara shiga - Hafsat Idris

To fah: Babu yarinyar da iyayenta za su yadda ta shiga harkar fim da sanin su, ko nima sai da na samu matsala da su kafin na fara shiga - Hafsat Idris

- Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, Hafsat Idris wadda a yanzu za a iya cewa tana sahun gaba a mata masu tashe ta tattauna da jaridar damokaradiyya

- Jarumar ta bayyana kalubalen da mata ke fuskanta yayin da suka bayyanawa iyayensu ko gidansu sha’awar fadawa harkar fim

- Ta bayyana cewa fim dai sana’a ce, kuma kowacce sana’a na da nagari da na banza

Fitacciyar jaruma a cikin masana’antar Kannywood, Hafsat Idris wadda a yanzu za a iya cewa tana sahun gaba a cikin matan da ake yayi a masana’antar, ta fadi yadda ta samu matsala a gidansu lokacin da ta bayyana bukatarta ta shigowa harkar fim a gidansu kafin daga baya su amince mata.

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da ake jin ta bakinta dangane da matsalar da wasu jarumai su ke samu a gida da zarar sun bayyana bukatar su ta shiga harkar fim.

Wasu daga baya iyayen nasu kan amince, yayin da wasu kuma basa samun amincewar ta su. Don haka ko dai su bari, ko kuma su ci gaba da yi ba tare da yardar iyayen nasu ba.

KU KARANTA: Innalillahi: Wani mutumi ya yiwa daliba fyade sannan ya kasheta ta hanyar caka mata wuka sau 52

Kamar yadda Hafsat Idris tace, “Dole ne duk wadda ta samu kanta a wannan halin, ‘yan gidansu su ji ba dadi. Amma daga karshe ina nuna musu, wannan harkar fim din sana’a ce. Sannan idan ka tafi yin shi, waya ma ba ka iya dauka balle ka samu damar zuwa yawo,”

“Kuma inaso mutane su sani, fim sana’a ce. Kuma kowacce sana’a akwai nagari da kuma na banza. Idan ka kama kanka, Allah zai taimake ka, saboda kai dai ka san me kake yi. Idan ka je da mutunci, zaka sameshi idan kuma akasin hakan ne, shima zaka samu.”

Daga karshe jarumar ta yi kira ga abokan aikinta da su kasance masu tsare mutuncinsu a duk inda suke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel