To fah: Dan ina fitowa a fim din Kudancin Najeriya ba yana nufin ni 'yar iska bace - Inji jaruma Amal Umar

To fah: Dan ina fitowa a fim din Kudancin Najeriya ba yana nufin ni 'yar iska bace - Inji jaruma Amal Umar

- Matashiyar jaruma Amal Umar ta kasance jarumar da take fina-finan Kannywood kuma tana yin na Nollywood

- Jarumar ta kalubalanci masu kallon masu wasan kwaikwayo a matsayin marasa tarbiya, ta ce tarbiya daga gida take

- Yawan fina-finan da take fitowa a masana’antar Nollywood sun danganci kalubalen da Arewacin Najeriya ke fuskanta ne

Matashiyar jaruma Amal Umar, ita kadai ce jarumar da ke fitowa a fina-finan Kannywoood kuma a lokaci daya take fitowa a fina-finan masna’antar Nollywood.

Jarumar matashiyar mai shekaru 20 kacal a duniya, ta kware sosai wajen wasan kwaikwayo. Hakazalika idan tana yaren turanci, dole ne abun ya baka sha’awa. Wannan dalilin ne kuwa ya bata damar samun wajen zama a masana’antar Nollywood .

Jarumar ta yi fina-finai na turanci da suka hada da MTV Sugar, Wings of a Dove, Up North da sauransu.

Wannan dalilin ne yasa mutane suka dinga cece-kuce a kan jarumar. Saboda dai duk jarumin hausa da ke fitowa a fina-finan masana’antar Nollywood, ana mishi wani kallo daban ne.

Jarumar ta ce, “Gaskiya abinda na sani kuma zan iya magana a kai shine, ko a fim din hausa, ana zaginmu kuma na kiranmu da ‘yan iska. Amma kuma mutane na manta cewa, tarbiya fa tarbiya ce. Duk yadda ka taso a gidanku, haka zaka fita waje kana rayuwa."

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga Barrack Obama da Sarauniyar Ingila su dawo addinin Musulunci na kakanninsu

“Toh ni dai na taso a gidan tarbiya, kuma koda na fara fim ban fuskanci kalubale ba, saboda duk inda naje ina tuna ni musulma ce. Kuma fina-finan kudu ko yaushe aka kira ni zan yi. A yanzu haka ina da fina-finai da yawa wadanda suke kan hanyar fitowa. Wasu kuma za a fara haska su a tashar Arewa 24 ba da dadewa ba.

“Yawancin fina-finan kudu da nake fitowa, ina fitowa ne wacce take taka rawa wajen abunda ya shafi rayuwar bahaushe. Kamar auren wuri da ake yi wa yara, doraawa yara talla da kuma auren dole. To duk ire-iren wadannan fina-finan su ne ake kirana. Don haka ko jibi aka kirani ko gobe, ni zan je.” In ji jarumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng