To fah: A shirye nake na auri kamaye a zahiri idan har zai yarda - Adama jarumar Dadin Kowa

To fah: A shirye nake na auri kamaye a zahiri idan har zai yarda - Adama jarumar Dadin Kowa

- Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Zahrau Saleh wacce aka fi sani da Adama ta ce a shirye take ta auri abokin aikinta Kamaye

- Ta bayyana cewa, aure nufin Allah ne kuma ba zata ki ba, idan har Allah ya hada kansu da abokin karawar nata

- Jarumar ta yi kira ga sauran jarumai da su hade kansu don gujewa rikice-rikicen da suka yi wa massana’antar yawa

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Zahrau Saleh wacce aka fi sani da Adama matar Kamaye, a cikin wasan kwaikwayon nan na Dadin Kowa, ta bayyana cewa a shirye ta ke ta auri abokin karawarta a wasan kwaikwayon. Asalin dai sunan Kamaye a zahiri ba a wasan ba, shine Dan azimi Baba Chediyar ‘Yar Gurasa.

A yayin wata tattaunawa da Adama ta yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano, jarumar ta ce: “shi aure lamari ne na Allah, kuma idan Allah ya rubuta cewa Kamaye mijina ne, to hakika sai na aureshi, kuma ba abin mamaki bane domin kuwa a shirye nake da na aureshi”.

Jaruma Adama ta kara da bayyana cewa, ita sam ba mafadaciya ba ce a zahiri. Kawai dai wasa ne aka bata tsarin ta fito a matsayin mafadaciya.

KU KARANTA: Queen Elizabeth: Sarauniyar Ingila ta gama shiri tsaf domin mikawa Yarima mai jiran gado karagar mulki

A karshe ta yi kira ga sauran jaruman massana’antar Kannywood din, da su taimaka wajen hada kansu tare da kaucewa rikice-rikece domin tabbatar da zaman lafiya, da cigaba ga jaruman da masana’antar baki daya.

Sau da yawa dai akan samu wasu tsiraru daga cikin jaruman fim su fara soyayya wacce har take kai su ga yin aure, kadan daga cikinsu sune irin su fitaccen jarumi Sani Musa Danja da matarsa Mansura Isah, wadanda har yanzu suke tare ba tare da samun wata matsala a bangaren auren na su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel