Ina son zama 'yar kasuwa kamar Dangote - Jaruma Sadiya Kabala

Ina son zama 'yar kasuwa kamar Dangote - Jaruma Sadiya Kabala

Jarumar fina-finan masana'antar Kannywood, Sadiya Kabala ta bayyana burinta a rayuwa. Jarumar ta ce bata da wani buri da ya wuce ta zama babbar 'yar kasuwa kuma maikudi kamar Alhaji Aliko Dangote.

Jaruma Sadiya Kabala ta wallafa hakan ne a shafinta na Instagram. Ta wallafa rubutun kamar haka: "Mafarki na shi ne in zama 'yar kasuwa kamar Dangote, nima wata kila akirani da 'Yargote'.

Wannan batun na jarumar ya jawo cece-kuce tsakanin mabiyanta na kafar sada zumuntar zamanin na Instagram. Mutane sundinga bayyan mabanbantan ra'ayoyinsu a kan rubutun. Tuni dai wasu suka fara mata fatan alheri, inda wasy suka fara kiranta da 'yargote.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da jaruman masana'antar Kannywood ke fatan zamowa 'yan kasuwa ba. Domin kuwa ko a baya-bayan nan matashiyar jaruma Maryam Yahaya ta bude shagon kasuwanci a Kano.

DUBA WANNAN: Damfarar $1m: Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta dakatar da ma'aikata 9

A wani cigaba kuma, daya daga cikin matasan jaruman masana’antar Kannywood, Rukayya Sukeiman Saje, wacce aka fi sani da Samira Saje, ta bayyana cewa kokarin dogaro da kanta ne yasa ta bar masana’antar shirya fina-finan.

Samira ta bayyana hakan ne a yayin bikin murnar bude sabon shagonta da aka gudanar. An yi bikin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba 2019 a sabon katafaren shagon da mai lamba 148, Titin Lawan Dambazau, daura da filin kasuwar duniya kuma kusa da shagon daukar hoto na Balancy da ke garin Kano.

Jarumar da ta bayyana yadda ta ke son samun hanyar dogaro da kanta, duk da kuwa ta kammala digirinta kuma har ta hidimtawa kasa. Ta ce, ta bar masana’antar ne don ta dogara da kanta tare da taimakawa wajen samar da abin yi ga ‘yan uwanta matasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel