Hanyoyi biyu da Tinubu zai iya samun takarar shugaban kasa a 2023

Hanyoyi biyu da Tinubu zai iya samun takarar shugaban kasa a 2023

Duk da kasancewar akwai sauran lokaci kafin kakar zaben shekarar 2023, tuni manyan 'ya'yan jam'iyyar APC sun fara kulle-kullen waye zai gaji Buhari idan ya kammala zangonsa na biyu.

Daga cikin wadanda ake kallon suna harin kujerar Buhari a 2023 akwai jagoran jam'iyyar APC na kasa, tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu.

Tinubu gogaggen dan siyasa ne da babu inda bashi da yara a fadin Najeriya. Tsohon gwamnan ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Buhari a zaben shekarar 2015 da 2019 da kuma kafa shugabancin jam'iyya na kasa da shugabancin majalisar tarayya da kuma sama wa wasu yaransa kujerar minista da sauran mukaman gwamnanati masu maiko.

Sai dai, tun kafin tafiya ta yi nisa, wasu manyan 'yan APC daga arewa sun fara nuna alamun cewa ba zasu bar mulki ya koma kudancin Najeriya ba. Ana ganin masu wannan bore na yin haka ne don ganin Tinubu bai samu takara ba, ala bar shi daga baya a sulhunta ya kawo dan takara, shi kuma ya cigaba da zama a matsayin jagoran jam'iyya kuma uba.

Wasu kuma na ganin cewa takarar Tinubu kan iya bawa jam'iyyar APC matsala wajen samun nasara a zaben 2023. Hujjar da suke kafa wa ita ce, Tinubu musulmi ne daga kudu kuma daukan Kirista a matsayin mataimaki daga arewa zai sa yakin neman zabe ya yi wahala, saboda yadda addini ke taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.

Amma masu burin Tinubu ya samu takarar shugaban kasa suna ganin cewa akwai hanyoyi biyu da gwaninsu zai iya samun tikitin takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Mutane sun caccaki Zahra Buhari a kan kudin shiga taron ganawa da ita da ta tsauwala

1. Alakarsa da shugabancin jam'iyyar APC na kasa: Ba boyayyen abu bane cewa Tinubu ne ya kawo karshen shugabancin tsohon shugaban jam'iyyar APC, Cif John Oyegun, tare da kafa Adams Oshiomhole.

Shugabancin jam'iyya yana taka muhimmiyar rawa wajen samun tikitin takara a kowanne mataki, sanin hakan ne yasa masoya Tinubu ke ganin cewa shugabancin jam'iyya a mataki na kasa zai bawa gwaninsu duk goyon bayan da yake bukata wajen samun tikitin takarar shugaban kasa a 2023.

2. Karfin tattalin arziki: Kudi na taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, hakan yasa jam'iyyu ke duba karfin tattalin arzikin 'yan takararta kafin bayar da tikitin takara, musamman a matakin kujerar shugaban kasa.

Ana hasashen cewa babu wani mamba a APC yanzu da zai jayayya da Tinubu ta fuskar karfin tattalin arziki, wanda hakan zai iya bashi damar samun tikitin takarar shugaban kasa, musamman idan PDP ta kara mika tikiti ga dan takara mai karfi kamar Atiku Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel