Damfarar $1m: Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta dakatar da ma'aikata 9
Hukumar kula da gidan gyaran hali, ta aminta da dakatar da manyan jami’anta 3 tare da wasu 6 a kan hannunsu da take zargi cikin damfarar dala miliyan daya da wani dan gidan gyaran hali yayi.
Francis Enobore, kakakin hukumar ya bayyana hakan ne a wata takardar da hukumar ta fitar a yau Laraba a Abuja.
Idan zamu tuna, shugaban hukumar gidajen gyaran halin, Ja’afaru Ahmed ya bada umarni yin gamsasshen bincike a kan zargin damfarar yanar gizo da aka aikata a gidan. Ana zargin wani wanda yake tsare a gidan gyaran halin na Kirikiri da ke Legas ne da aikata laifin tare da hadin guiwar jami’an.
DUBA WANNAN: Rusau: Hotunan gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, shugaban hukumar gidajen gyaran halin ya tabbatarwa da jama’a cewa duk wanda aka kama da hannu a taimakawa wajen wannan aika-aikar, ba zai tafi haka babu hukunci ba. Dole ne ya fuskanci fushin hukuma.
Damafarar da ake zargin wani mutum mai suna Hope Aroke da aikatawa yayin da yake tsare, ta jawo ayar tambaya a kan yanayin cin hanci da yayi katutu a gidajen gyaran halin kasar nan.
Enobore yace, shugaban ya mika amincewar dakatar da jami’an ne don tabbatar da an kawo gyara fannin shugabancin gidajen. Ya kara da jaddada cewa, hukumar a shirye take da ganin ta tsince masu karanci dabi’a da nagarta daga zama jami’anta
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng