Matar aure ta kashe mijinta ta hanyar matse masa 'mazakuta'

Matar aure ta kashe mijinta ta hanyar matse masa 'mazakuta'

Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Edo sun kama wata mata, Eki Ekhator, mai tsaka-tsakin shekaru, bisa zarginta da kashe mijinta ta hanyar yi masa mugun riko a mazakutarsa.

Lamarin ya faru ne a garin Ukhiri da ke yankin karamar hukumar Ikpoba - Okha a jihar.

Majiyar jaridar The Nation ta sanar da ita cewa an samu rikici a tsakanin ma'auratan bayan matar ta zargi mijinta da cin amanarta.

The nation ta rawaito cewa majiyarta ta sanar da ita cewa ma'auratan yawan yin fada, musamman duk lokacin da mijin ya dawo gida da daddare a makare.

Ko a ranar da karar kwana ta fada kan mijin, sai da ma'auratan suka yi fada, lamarin da yasa matar ta yi wa marigayin mugun riko a 'mazakutarsa' bayan ya mare ta a lokacin da suka fara fada.

DUBA WANNAN: Gwamnonin APC 3 da kan iya gadar Buhari a 2023

A cewar majiyar, nan take mijin ya fadi sumamme sakamakon tsananin rikon da matar ta yi masa a 'mazakuta' kafin daga bisani likitoci su tabbatar da cewa ya mutu bayan an kai shi asibiti.

Yanzu haka jami'an rundunar 'yan sanda na musamman da ke bincike a kan kisan kai sun fara gudanar da bincike a kan kisan.

Wata majiya a hedikwatar 'yan sanda ta ce matar ta dora alhakin faruwar lamarin a kan sharrin shaidan.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwabuzor, ba a kan faruwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel