Ba harkar fim ce ta hanani zaman gidan aure ba - Inji Fati KK bayan an ganta a wani sabon fim

Ba harkar fim ce ta hanani zaman gidan aure ba - Inji Fati KK bayan an ganta a wani sabon fim

- Tsohuwar fitacciyar jarumar Kannywood, Fati KK ta dawo fim a karo na biyu bayan mutuwar aurenta

- Jarumar ta bayyana dalilin dawowarta da cewa, bata da wata sana’ar da ta fi mata harkar fim

- Ta musanta zargin mutane da suke tunanin ta kasa zaman aure, kuma tace ba wani abu bane don ta dawo fim

Fitacciyar jaruma Fatima Sadisu wacce aka fi sani da Fati KK, ta bayyana cewa ta dawo harkar fim ne don bata da wata sana’ar da ta fi ta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin da take tattaunawa da wakilin northflix.ng, dangane da dawowarta harkar fim bayan mutuwar aurenta, kuma hakan ba shine na farko da tayi ba.

Domin ko a shekarun baya, jarumar tayi aure. Bayan mutuwar auren kuma ta kara dawowa harkar fim aka ci gaba da damawa da ita. Ana cikin hakan kuwa sai ta kara yin auren. Yanzu haka kuma gashi ta kara fitowa ta kuma dawowa harkar fim gadan-gadan.

A tambayar da aka yi wa jarumar game da nasarorin da ta samu a Kannywood, ta amsa da cewa, “Ba ni da wani abin cewa sai sai in ce Alhamdulillahi. Kuma InshaAllahu muna fatan alheri a ciki. Dama can sana’armu ce, aure ne ya raba mu. Yanzu kuma da babu auren mun dawo, ka ga ai ba wani abu bane. Kuma na tsinci harkar kamar yadda na barta, kuma ina fatan Allah ya zaba mana abinda yafi alheri.”

KU KARANTA: Duk jarumar da ta ce harkar fim yafi zaman aure, tana cikin wahala - Halima Atete

“Amma maganar dawowa fim, gaskiya sai a hankali. Saboda zaka ga wasu ba za su fahimce ka ba. Amma sana’ar ka sana’ar ka ce. Komai lalacewarta taka ce, baka isa ka zage ta ba, saboda da sana’ar aka san ka, da ita ka daukaka, da sana’ar ka ke rufawa kanka asiri.”

Ta cigaba da cewa, “Amma yanzu mutane suna ganin auren Fati na daya ya mutu, ta kuma kara yin wani ya mutu, ta kuma sake dawowa fim. Abinda zasu fada, shi ne, ai daman ba ta son zaman auren. Fim din ne ya dauke mata hankali, wanda kuma ba haka bane wallahi.”

“Amma ni yanzu gaskiya zabin Allah nake nema, don haka duk abinda Allah ya zabawa rayuwata, ina fatan ya zama alheri a gareni. A cikin harkar fim, ba wani sabon abu bane auren mace ya mutu kuma ta dawo,” a cewar jarumar.

Sai dai masu lura da harkar fim din sun gano cewa, duk macen da tayi aure ta dawo harkar, bata kara tasiri. Saboda sabbin jaruman da ake samu koyaushe sun sha gabansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng