Duk jarumar da ta ce harkar fim yafi zaman aure, tana cikin wahala - Halima Atete

Duk jarumar da ta ce harkar fim yafi zaman aure, tana cikin wahala - Halima Atete

- Jaruma Halima Atete ta kasance shahararriyar jaruma mai jan zarenta a masana’antar kannywood a baya

- Lokaci daya jarumar ta yi batan dabo, wanda har hakan yasa aka fara tunanin ko tayi aure

- Jarumar ta ce duk lokacin da aure yazo, a shirye take a matsayinta na Musulma kuma ‘yar sunnah

An dade ba a ganin jaruma Halima Atete a cikin harkar fim, duk da kuwa jarumar ta kasance babbar jaruma mai jan zarenta a baya. Halima Atete ta kai kololuwar da ya zamo ita kadai ake magana a cikin jaruman masana’antar mata.

Amma kuma lokaci daya sai ta bace babu amo balle labarinta. Wannan dalilin ne yasa jama’a suka fara tambayar cewa ko jarumar ta yi aure ne? Wannan dalilin ne yasa wakilin jaridar Damokaradiyya ya nemi jin ta bakin jarumar.

“Ina nan daram a harkar fim, kuma ina gudanar da harkokina kamar yadda aka sani. Sai dai kowa ya san cewa ita harkar fim a yanzu ba kamar lokacin baya bane. A don haka, ko ba a ganin mutum, a sani cewa harkar ce ta zo da haka. Dole ne kuwa mutum ya nemi wata hanyar don rufin asirinshi.” In ji Atete.

KU KARANTA: Tirkashi: Fasto ya shiga tsaka mai wuya bayan matar da ya gayyata taje gidanshi ta mutu jim kadan bayan ya kammala zina da ita

Da aka tambayi jarumar ko ya batun aure? Sai tace, “Rashin ganina da masoya na suka yi, har suka fara zaton ko nayi aure ne, babban fatan alheri ce. Ina nan ba aure nayi ba amma ina jira lokaci. Ni ‘yar sunna ce, don haka ba zan ki sunna ba. Duk lokacin da aure kuwa ya zo a shirye nake, ko kaine ka shirya ka fito,” Atete ta ce.

“Idan aure ya zo, kawai yinshi ne mafi alheri. Babu amfani a ce wai don kina fim sai ki ki yin aure. Duk kuwa mace da tace fim yafi mata aure, toh tana cikin wahala. Don haka nake shawartar matan masana’antar Kannywood masu irin wannan tunanin da su canza.” Atete ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel