Gwamnatin Yari ta saye makamai 8, 000 ta ba ‘Yan sa-kai – Inji Matawalle

Gwamnatin Yari ta saye makamai 8, 000 ta ba ‘Yan sa-kai – Inji Matawalle

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya sake magana a game da gwamnatin da ya gada, ya ce Abdulaziz Yari ya dauki jami’an tsaro 8, 000 aiki wanda ya sa sha’anin tsaron jihar ya cabe.

Mai girma gwamnan ta bakin Darektan hulda da jama’a. ya ce ma’aikatan tsaro na ‘yan sakai da aka dauka, har aka saya masu makamai sun jagwalgwala halin zaman lafiya a jihar a baya.

Malam Yusuf Idris ne ya yi wannan jawabi a madadin gwamnan a Ranar Lahadi, 25 ga Watan Nuwamba. Idris ya yi wannan bayani a lokacin da ya kira wani taro da Manema labarai a jihar.

Darektan hulda da jama’a na Zamfara, ya bayyanawa ‘yan jarida cewa wadannan Dakaru na ‘Yan sakai da tsohon gwamnan ya kirkira, ya ke biyan albashi, ya sayawa makamai su ke tada rikici.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a matsayin martani ga jawabin da jam’iyyar APC ta yi ta bakin tsohon Jigonta, Ibrahim Dan Maliki Gidan Goga, ta na kare tsohon gwamnan na ta a Zamfara.

KU KARANTA: Abin da na yi bayan kotu ta hana ni zama Gwamnan Zamfara - Koguna

A cewar Dan Maliki Gidan Goga, wanda ya wakilici tsohon gwamna, Abdulaziz Yari, sabuwar gwamnatin PDP ta Bello Matawalle, ta na yaudarar jama’a ne da cewa an daina kashe-kashe.

A raddin gwamna mai-ci ya ce: “Ka da ku manta cewa a lokacin da ake rikici a 2013, lokacin Abdulaziz Yari ya na gwamna, ya saye mamakai ya ba kungiyar da su ka gagari hukuma.”

Matawalle ya kara da cewa: “Yanzu za ayi mamakin ina wadannan makamai su ka shige. Shi dai Yari ne ya dauki hayar ‘Yan sa-kai 80000, wanda yanzu ta tabbata su ke kai sababbin hare-hare.”

Gwamnan na PDP ya ce a lokacin Yari ya na gwamna ne aka kai hari a Kauyen ‘Yargaladima a Garin Magu aka kashe jama’a, amma ya buga ya bar Najeriya jim kadan bayan ya leka Kauyen.

“Haka ya faru har sai da aka roke shi ya dawo gida lokacin da aka kashe mutane Birane, Kizara da sauransu, Yari ya bi gwamnoni ya tafi Daura sa’ilin da abin ya faru. Bai da lokacin mutanensa”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel