Zaben Bayelsa: Jonathan ya mayar wa da Sule Lamido martani

Zaben Bayelsa: Jonathan ya mayar wa da Sule Lamido martani

Goodluck Jonathan ya mayar da martani ga Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa a kan ikirarin da yayi na cewa ya goyi bayan APC ne a zaben jihar Bayelsa. Lamido ya ce tsohon shugaban kasar ya yi hakan ne don ya kubcewa zarginsa da ake a kan almundahanar kwangilar Malabu.

Kamar yadda mai magana da yawun Jonathan, Ikechukwu Eze, ya sanar, yace tsohon gwamnan ya shirya karya ne kawai. Tsohon shugaban kasar yace, bai san dalilin da yasa tsohon gwamnan ya tsoma bakinsa a lamarin ba. Duk da kuwa zancensa cike yake da tantama tare da karairayi, jaridar The Cable ta ruwaito.

Jonathan ya cigaba da cewa, Lamido ba shi da tabbaci ko matsaya a duk zarginsa. Kamar yadda tsohon shugaban kasar ya sanar, "A lokaci daya, Lamido ya zargi cewa Jonathan ya ci amanar jam'iyyarsa saboda yana matukar fushi da gwamna Dickson,".

DUBA WANNAN: Kungiyar kamfen din Buhari ta yi martani a a kan sake tsayawarsa takara a karo na uku

A wani ikirari kuma, Lamido yace "Jonathan ya ci amanar jam'iyyarsa ne saboda ya san matsalar da ke tsakaninsa da Buhari da gwamnatinsa. Sai kuma matsalar Malabu, ina tunanin ta taka rawa".

Idan zamu tuna, jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda zauren dattawan jam'iyyar PDP suka zargi Jonathan da musayar nasarar jam'iyyarsa a jihar Bayelsa. A kan haka ne suka yi kira ga jam'iyyar da ta ladabtar da tsohon shugaban kasar.

Zauren dattawan jam'iyyar PDP din ya bayyana yadda jam'iyyar ta yi wa Jonathan halaccin da bata yi wa kowa ba a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel