Babu zancen son kai: Ni da Ali Nuhu mune babbar matsalar masana'antar Kannywood - Adam A Zango

Babu zancen son kai: Ni da Ali Nuhu mune babbar matsalar masana'antar Kannywood - Adam A Zango

- Fitaccen jarumin nan na amsana’antar kannywood, Adam A. Zango ya bayyana silar rikice-rikcen da suka yawaita a masana’antar Kannywood

- Ya ce silar rikicin kuwa ba komai bane face yaransa da kuma yaran jarumi Ali Nuhu, wanda ya dora alhakin laifin a kan jarumi Ali Nuhu

- Ya ce, tsawatar wa da yaran nasu zai iya kawo maslaha ga masana’antar, duk da dai shi baya barin yaransa su ci wa kowa mutunci

Shahararren jarumin masana’antar Kannywood kuma mawaki, Adam Zango, ya bayyana silar rikicin da ke addabar masana’antar Kannywood. Ya zargi yaranshi da kuma yaran jarumi Ali Nuhu da rura wutar rikicin da taki ci takic cinyewa a masana’antar ta Kannywood.

A wata tattaunawar da jarumin ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano, ya bayyana irin rikicin da yaransa tare da yaran jarumi Ali Nuhu ke haifarwa a masana’antar Kannywood. Inda kuma ya kara da cewa babu shakka hakan laifin jarumi Ali Nuhu ne.

Kamar yadda jarumin ya ce, da suna tsawatar wa da yaran nasu, da wadannan rikice-rikicen basu dinga yawaita a masana’antar ba.

KU KARANTA: Tirkashi: Zpretty ta caccaki 'yan soshiyal midiya

Jarumi Adam Zango yace, ta bangarenshi yana tsawatar wa da yaranshi, don bai yarda yaran na shi su ci zarfin wani ko wata ba.

Idan ba zamu manta ba, a kwanakin baya jaruman biyu sun tafka wani rikici wanda sai da ya danganta su da zuwa kotu, sannan daga bisani aka samu aka yi sulhu a tsakaninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng