Tirkashi: Zpretty ta caccaki 'yan soshiyal midiya

Tirkashi: Zpretty ta caccaki 'yan soshiyal midiya

- Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood, Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota tsegumi a kafafen sada zumuntar zamani

- Jarumar ta wallafa bidiyo a shafinta na Instagram ne inda ta ke magana a kan masu bata wa jaruman masana’antar suna

- Ta yi gargadin cewa, zata iya daukar mataki a kan duk wanda ta kama da laifin bibiyar lamurranta tare da bata mata suna

Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood, Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota amfani da kafafen sadarwa ta zamani.

A wani bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ta yi suka ga wadanda suka kware wajen bibiyar lamuranta da na sauran jarumai abokanan sana'arta. Wadanda daga zarar sun ga jarumi ko jaruma ta wallafa sabon hoto, zasu fara yadawa tare da tsokaci a kai.

Jarumar ta yi kausasan kalamai na musamman ga masu wallafa bayanai a dandalin YouTube, inda ta ce mafi yawansu basu da aikin yi face shirya karya da gulma, don batawa jaruman masana’antar Kannywood suna a idon duniya.

KU KARANTA: Allah mai iko: Mace ta farko a duniya makauniya kuma kurma da ta zama likita

Jarumar ta yi wata barazana inda ta ke cewa, “Ku kiyaye ni, zan fa iya yin wani abu a kan duk wanda na samu da bibiyata ta irin wannan sigar”.

Kawo yanzu dai, sama da mutane dubu biyu ne suka kalli wannan bidiyon na jarumar. Sama da mutane dari kuwa sun yi tsokaci a kai.

Da yawa daga cikin jaruman masana’antar da suka yi tsokaci a kan gargadin, sun yi ta bata hakuri ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel