Hotunan ziyarar da shugabannin darikar Tijjaniyya suka kaiwa Buhari
A cigaba da gudanar da bukukuwan Mauludi da mabiya darikar Tijjaniya ke yi a fadin Najeriya da wasu sassan nahiyar Afrika, shugabannin darikar sun ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa.
Shugabannin darikar sun ziyarci shugaba Buhari a ranar Litinin a fadarsa da ke Abuja a bisa jagorancin shugabansu Shaikh Muhammad Lamin.
Wannan ba shine karo na farko da shugabannin darikar suka ziyarci shugaba Buhari, ko a lokacin bikin mauludin shekarar da ta gabata sun kai wa shugaba Buhari a fadarsa.
Ziyarar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da ake musayar yawu tsakanin wasu mabiya Tijjaniyya da 'yan kungiyar JIBWIS; da aka fi sani da Izala, a kan ziyarar da shugabannin kungiyar suka kai fadar shugaban kasa domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Asali: Legit.ng