Adamawa: An kashe Jama’a da-dama a ta’adin Makiyaya a Shuwa-Kalaa

Adamawa: An kashe Jama’a da-dama a ta’adin Makiyaya a Shuwa-Kalaa

Mutane birjiki da ke zaune a wani Kauye da ake kira Shuwa-Kalaa da ke karamar hukumar Hong, a jihar Adamawa, ake tsoron sun mutu a halin yanzu, a sakamakon wani harin Makiyaya.

Wata Jaridar kasar nan ta rahoto cewa an hallaka mutane da-dama ne a harin da aka kai Ranar Asabar, 23 ga Watan Nuwamban 2019. Makiyayan sun dade su na shiga wannan Yanki.

Wani wanda abin ya auku a gaban idanunsa, ya shaidawa Manema labarai cewa wadannan Makiyaya sun afkawa Kauyen Shuwa-Kalaa jiya ne, inda su ka shiga buda wuta ko ta ina.

Wannan Bawan Allah ya ke fadawa ‘yan jarida cewa da yawan mutane sun tsere daga Kauyen yayin da aka fara harbe-harbe domin su tsira da rayukansu, yayin da aka ritsa da wasu.

A cewar wani wanda ya bada shaida, tun farkon lokacin kaka, wadannan Makiyaya su ka fara addabar Kauyen. Ya ce a Ranar Asabar ne su ka tare da wani mutumi bayan ya yi girbi.

KU KARANTA: Boko Haram: Gwamnan Borno ya yi hayar 'Yan sintiri daga ketare

"Da safen nan (Ranar Asabar) wadannan mutane (Makiyaya) su ka kai wa wani mutumi hari bayan ya ciro kayan amfani daga gona zai kawo gida. Sai ya dawo cikin gari ya sanar da mu.

"Dawowarsa ke da wuya, sai mu ka hangi wadannan Makiyaya sun dumfaro mu ko ta ina. ‘Yan banganmu sun yi kokarin hada gayya domin kare kanmu, kuma mu ka yi nasarar tare su."

Duk da wannan kokari da Mazaunan Shuwa-Kalaa su ka yi, an yi rashin sa’a an kashe mutane. Wanda ya bada shaidar ya fadawa ‘yan jarida cewa an kashe mutane daga kowane bangare.

Mutanen wannan Kauye sun bayyana cewa Sojoji sun taimaka wajen fatattakar Makiyayan. Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, bai iya cewa komai game da harin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel