Iyalan Maina sun kalubalanci alkalin da ke shari'ar, sun bukaci a sauyashi

Iyalan Maina sun kalubalanci alkalin da ke shari'ar, sun bukaci a sauyashi

Iyalin Abdulrasheed Maina sun yi kira ga shugaban babban kotun tarayya,Jastis John Tsoho a kan ya canza alkalin da ke shari'a tsakanin gwamnatin tarayya da Faisal Abdulrasheed Maina. Iyalin sun ce, basu da kwarin guiwa a kan Jastis Okon Abong na babbar kotun tarayya ta 6 da ke Abuja.

Iyalin sun bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsu, Usman Abdullahi, cewa sun shigar da bukatar sauyin alkalin domin tsoron yuwuwar rashin adalci da Faisal Maina zai iya fuskanta.

"Biyo bayan bukatar da iyalan Maina suka tura ta hannun lauyan su, akwai bukatar babban alkali, Jastis John Tsoho da ya maida shari'ar zuwa hannun wani alkali banda Jastis Okon Abang don akwai yuwuwar Faisal ba zai samu adalci ba,

DUBA WANNAN: Pantami ya samu lambar yabo

"Wannan bukatar kuwa ta biyo bayan yadda alkalin ke nunawa ta aikinsa. Akwai yuwuwar dakile hakkin Maina a sakamakon hakan,"

A maida martanin alkalin, wanda wata majiya wacce ta bukaci a boye sunanta tace, alkalin ya yi kokarin musanta abinda ake zarginsa a kan Maina. Kawai wannan kokari ne na ganin yadda za a maida shari'ar hannun alkalin da zasu iya juyawa yadda suke so, cewar alkalin.

Iyalan Maina sun zargi alkalin da bayyana tsanar mahaifin Faisal tare da nuna masa hantara a ranar 25 ga watan Oktoba 2019. Alkalin ya bukaci Abdulrassheed Maina da ya daina kallonsa a dakin kotu, hakan ya nuna yadda tsanar Maina ta yi tasiri a zuciyarsa.

"Wannan abun ya zama babbar barazana ga Maina da lauyoyinsa, wadanda suka fara zaton za a yanke musu hukuncin da ba zai yi musu dadi ba. Hakan kuma ya sa sun fara tunanin ba za a yi musu adalci ba." Cewar iyalin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel