Hotunan wasu takalman Buhari da ya dauki hankulan 'yan Najeriya a Twitter

Hotunan wasu takalman Buhari da ya dauki hankulan 'yan Najeriya a Twitter

Wani ma'abocin amfani da shafin sada zumunta na Twitter @DoubleEph ya wallafa wasu hotunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari sanye da wasu bakaken takalma da ya yi ikirarin cewa samfarin 'Bottega' ne wanda a kalla kudinsu ya kai fam 535 da ya yi dai-dai na N246,100.

Har ila yau ya sake wallafa wani hoton shugaban kasar tare da wasu mutane inda a nan ma aka gano wani takalmi mai kama da samfurin ta Bottega sai dai wannan launin ruwan kasa ne ba baki ba wadda hakan na nuna akwai yiwuwar ba guda daya shugaban ke da shi ba.

Wannan hotunan sun janyo hankulan mutane masu amfani da shafin Twitter masu yawa inda suka rika bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu kan batun.

Cikin wanda hankalinsu ya kai ga hotunan har da hadimin Shugaban kasa a fannin sabbin kafafen watsa labarai Bashir Ahmad wadda ya kasa cewa komi kan hotunan sai dai nuna mamakinsa da cewa 'Wow'.

@DoubleEph ya wallafa wasu hotunan Shugaban kasar tare da iyalansa wato dansa Yusuf, matarsa Aisha da diyarsa a cikin jirgin sama inda nan ma ya yi nuni da cewa diyar shugaban kasar tana sanye da takalmi ne samfurin na Bottega.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa fusatattun shugabannin APC suka nema Oshiomhole ya sauka kujerarsa

Wasu wadanda suka yi tsokaci kan hotunan sun nuna cewa takalman da shugaban kasar ya saka ba Bottega bane idan har mutum ya lura da yanayin takalman biyu yayin da wasu kuma suka nuna cewa ba wata matsala bace idan shugaban kasa mai arziki irin Najeriya ya saka takalmin da farashinsa ya tasanma N246,000.

Wannan dai ba shine karo na farko da 'yan Najeriya ke magana kan abubuwan da Shugaban kasa ko iyalansa ke amfani da su ba da niyyar nuna cewa suna 'cin duniya da tsinke' yayin da sauran 'yan Najeriya ke fama da yadda za su samu abin kaiwa baka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel