Magana daga bakin mai ita: Buhari yace baya sha’awar zarcewa a mulki karo na 3

Magana daga bakin mai ita: Buhari yace baya sha’awar zarcewa a mulki karo na 3

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da sha’awar zarcewa a kan karagar mulkin Najeriya a matsayin shugaban kasa da sunan neman wa’adin mulki na uku.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wanda ke gudana a yanzu haka a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa dake babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Blue Print ta ruwaito.

KU KARANTA: Mutumin daya zane jami’an kiyaye haddura guda 2 ya ga ta kansa a gaban Kotu

Wannan batu na shugaban kasa ya karyata rade radin da wasu yan siyasa ke yin a cewa shugaba Buhari na neman zarcewa da wa’adin mulki na uku kamar yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi, inda wasu ke zargin Buhari na wannan shiri ne da hadin bakin yan majalisu.

A jawabinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar ma mahalarta taron cewa zai tattara inasa inasa ya bar fadar gwamnatin Najeriya zuwa shekarar 2023 a karshen wa’adin mulkinsa na biyu saboda kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta neman wa’adin mulki na uku.

Buhari ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar APC dasu mayar da hankali a mazabunsu, tare da tabbatar da sun mamaye mazabunsu a siyasance ta yadda zasu zama masu fada a ji, domin kuwa abin kunya ne a ce APC ta rushe bayan karewar wa’adin mulkinsa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon shugaban wucin gadi na jam’iyyar APC, Bisi Akande, gwamnoni da sauran manya manyan jiga jigan jam’iyyar.

A wani labarin kuma, wani fitaccen malamin addinin kirista kuma fitaccen dan siyasa a jahar Edo, Fasto Aimola John ya yanke jiki ya fadi jim kadan bayan ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC tare da maigidansa Osagie Ize-Iyamu.

Shi dai Ize-Iyamu wanda shine tsohon dan takarar gwamnan jahar Edo a zaben shekarar 2016 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya sauka sheka zuwa APC ne a ranar Alhamis, tare a tawagar magoya bayansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel