Yan majalisa za su yi ma dokar N-Power garambawul domin ta kunshi matasan NYSC

Yan majalisa za su yi ma dokar N-Power garambawul domin ta kunshi matasan NYSC

Majalisun dokokin Najeriya zasu fara gudanar da gyaran fuska ga dokokin da suka samar da tsarin bada tallafi na gwamnatin tarayya ta hanyar daukan matasa aiki na N-Power ta yadda za ta kunshi har da matasa yan bautan kasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban kwamitin majalisar wakilai dake kula da matasa da wasanni, Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana haka yayin da kai ziyara zuwa sansanin yan bautan kasa dake Wanune, cikin karamar hukumar Tarka na jahar Benuwe.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige basaraken gargajiya a jahar Katsina

Dan majalisa Adeyemi ya shaida ma yan bautan kasa cewa majalisa za ta gudanar da gyaran fuska ga dokokin da suka samar da N-Power ta yadda yan bautan kasa ma zasu fara amfana da shi, haka zalika ya yi kira matasan su rungumi tsarin koyar da sana’ar hannu na SAED.

Haka zalika dan majalisan ya yi kira ga hukumomin gwamnati da kamfanoni da cewa kada su kuskura su ki karbar yan bautan kasa idan har aka turasu yi ma kasa hidima a wadannan wurare. Sa’annan ya roki gwamnatin jahar Benuwe ta fara biyan yan bautan kasa dan wani abu a duk wata domin karfafa musu gwiwa.

A nasa jawabi, shugaban NYSC reshen jahat Benuwe, Shichi Joshua Simon ya bayyana ma kwamitin majalisar cewa suna bin tsarin bayar da horo ga yan bautan kasa sau da kafa a sansaninsu, inda yace hakan zai kara hadin kai tsakanin matasan.

Daga karshe Mista Shichi ya bayyana gamsuwarsa da yadda matasan suka gudanar da kansu a sansanin, inda yace tun shigarsu sansanin sun nuna ladabi da biyayya tare da nuna kwazo a duk ayyukan da ake yi a sansanin.

A wani labari kuma, babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya gudanar da gyara a tsohuwar makarantar firamarin da ya yi, LEA Unguwar Sarki Kaduna, sa’annan ya baiwa makarantar kyautan littafan karatu guda 1,000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: