Kotun Shari'a: Zan biya shi sadakin da ya bayar matukar ya biya ni bashin da nake binsa - Matar aure

Kotun Shari'a: Zan biya shi sadakin da ya bayar matukar ya biya ni bashin da nake binsa - Matar aure

Wata kotun shari’a da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, a ranar Alhamis ta raba aure tsakanin Sani Ahmad da Maryam Aliyu a kan wani sabani da suka gaza sasantawa.

Alkalin, Murtala Nasir, ya kuma umurci mai karar da ta maidawa mijin nata sadakin N45,000 da ya biya tunda ita ce ta nemi a raba auren.

Da farko Maryam Aliyu, mai kara, wacce ke zama a Yankin Tudun Wada na Kaduna, ta fada ma kotu cewa tana son a rana aurensu ta hanyar Khul’i.

Maryam ta ce a shirye take da ta mayar da sadakin da ta amsa daga wajen Ahmad.

Sai dai kuma ta roki kotun da ta taimaka ta amso mata bashin N37,000 da take bin mijin nata da kuma wani bashin N8,000 na abincin yara na watannin Oktoba da Nuwamba.

A nashi bangaren, wanda ake karan, wanda ya kasance mazaunin unguwa guda da mai karar, ya ce ya amince da bukatar matarsa, inda ya kara da cewa dama ya yi mata saki biyu a baya.

Wanda ake karan ya kuma yarda cewar mai karar na binsa bashin kudin da tace.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta baiwa Yahaya Bello takardar shaidar cin zabe

Alkalin ya yanke hukunci cewa wacce ke karar ta biya sadakin N45,000 ta hanyar juyawa da bashin da take bin wanda ake kara na 37,000 da kuma N8,000 na abincin yaransu. Sannan ya raba auren.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kama wani matashi, Mudasiru Tanimu, mai shekaru 18, bisa zarginsa da zuba guba a cikin abin sha da aka raba a wurin wani biki a kauyen Barhim da ke yankin karamar hukumar Batagarawa a jihar.

A cikin wani jawabi mai dauke da sa hannun kakakinta (PRO), SP Gambo Isah, da ta fitar a ranar Alhamis, rundunar 'yan sandan jihar ta ce Tanimu ya hada kai da wani matashi, Nafiu Umar, mai shekaru 18 domin saka gubar a cikin abincin 'yan bikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel