Bankuna za su ja daga da NUBIFIE kan shirin korar Ma’aikata a Najeriya

Bankuna za su ja daga da NUBIFIE kan shirin korar Ma’aikata a Najeriya

The Sun ta rahoto cewa kungiyar NUBIFIE ta ma’aikatan bankuna da hukumomin tattalin arziki, ta gargadi wani banki a game da shirin da ya ke yi na sallamar ma’aikatansa kwanan nan.

Wannan kungiya mai kare hakkin ma’aikatan banki ta ce za ta rufe gaba daya rassan wannan banki da ke fadin Najeriya, muddin aka ki janye yunkurin fatattakar mutane 1000 daga aiki.

Kungiyar ta fadawa ‘ya ‘yan ta cewa ka da su karbi takardar sallama daga aiki har sai idan ta amince da matakin. Shugaban wannan kungiya na kasa, Anthony Abakpa, ya bayyana wannan.

Mista Anthony Abakpa ya fadawa ‘Yan jarida a lokacin da su ka tuntube sa a waya cewa bankunan sun shirya tsaf domin korar ma’aikata rututu daga aiki ba tare da bin doka ba.

“Mun samu labari cewa wani banki (tare da boye suna) zai rabawa ma’aikatansa sama da 1, 000 takardar sallama a safiyar yau (21 ga Watan Nuwamban 2019) ba tare da mun zauna ba.”

Abakpa ya ce bankin ya kammala shirin korar ma’aikatan ne ba da amincewar NUBIFIE ba. A ka’ida, ya kamata ace an yi zaman cin ma yarjejeniya tsakanin kungiyar ma’aikatan da bankin.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta yarda a kara harajin VAT a Najeriya

A cewar Abakpa, kungiyar da ya ke jagoranta ta NUBIFIE za ta dakatar da aikin wannan banki a kaf fadin kasar nan saboda ta na ganin cewa matakin da aka dauka ya sabawa ka’idar kwadago.

“Ba za mu yarda da duk wani danyen aiki da ya sabawa dokokin kwadago ba, domin kuwa ba za mu taba goyon bayan abin da ya ci karo da ra’ayin ma’aikatanmu ba. Inji Anthony Abakpa.

“Mun yi amanna da sulhu da kuma yarjejeniya ta lalama. "Dalilin haka ne shugaban kungiyar ma’aikatan ya ce sun sanar da kungiyar kwadago da ma’aikatar kwadago game da lamarin.

Haka zalika NUBIFIE ta sanar da babbar yayarta watau ASSBIFI a kan nuna rashin goyon baya game da tsige jama'a kwatsam. Kungiyar ta ce dola a biya jama’a hakkokinsu kafin a kore su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng