Abin da ya sa mu ka fatattaki Yaran da ke cikin bidiyon batsa – BABCOCK

Abin da ya sa mu ka fatattaki Yaran da ke cikin bidiyon batsa – BABCOCK

Jami’ar nan ta BABCOK ta tabbatar da sallamar Matashi da Budurwar da su ka bayyana a wani bidiyon batsa. Tuni dai wannan bidiyo ya yada gari inda aka ga ‘yan makarantar a wani yanayi.

Hukumar makarantar ta ce ta kori wadannan ‘Dalibai duk da cewa ba a cikin harabar ta aka yi wannan danyen aiki ba. Jami’ar ta ce ta kori ‘Daliban ne saboda dokoki da kuma ka’idojinta.

Darektan sadarwa da kasuwanci na jami’ar, Joshua Suleiman, shi ne ya yi magana a madadin makarantar inda ya ce an dauki wannan bidiyo ne a Afrilun 2019 bayan ma an kori shi Saurayin.

Tun Watan Fubrairun bana, Jami’ar BABCOCK ta sallami Saurayin da ya fito a cikin bidiyon, bayan an yi dogon bincike an same sa da yin ba daidai ba, kamar yadda aka san makarantar nan.”

KU KARANTA: Jami'in sharia' zai tafi gidan kurkuku bayan ya nemi cin hanci da rashawa

Ya ce: “Buduwarsa ce a cikin wannan bidiyon, kafin a fito da faifen, ‘Dalibar sashen ilmin Akawu ce a jami’ar nan. Bayan bincike, an kore ta daga jami’ar a dalilin sabawa dokoki da ka’idoji.”

“Kamar yadda ta fadawa hukuma da kanta, wannan abu ya faru ne a asibitin St Bridget da ke Garin Abeokuta, a lokacin da ake kokarin a shawo kan matsanancin shaye-shayen Matashin.”

Darektan jami’ar ya ce Matasan sun yi wannan aiki ne a lokacin da yarinyar ta ziyarce sa a asibiti a jihar Ogun lokacin da aka yi hutun makaranta. Ya ce wannan ya nuna tabarbarewar al’umma.

A wannan jawabi da ya fito Ranar 20 ga Nuwamba, Makarantar ta kara bada tabbacin cewa za ta cigaba da kokari na ganin ta dabbaka tarbiyyar da ta dace tare da kuma bada ilmi mai nagarta.

Jami’ar da ke Ilishan-Remo a yankin Irepodun da ke karamar hukumar Ikenne a jihar Ogun ta na aiki ne da koyarwar addini. Jami’ar ta na karkashin wani coci ne mai suna 7th-day Adventist.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel