Musulunci ya samu karuwa: Ambasadan Birtaniya dake kasar Saudiyya ya Musulunta tare da matarshi

Musulunci ya samu karuwa: Ambasadan Birtaniya dake kasar Saudiyya ya Musulunta tare da matarshi

- Allah mai shiriya a lokacin da yaso ne ya shiryar da jakadan Birtaniya dake kasar Saudiyya

- An ga hoton Simon Collins da matarshi sanye da harami kuma a gaban ofishin jakadancin Birtaniya da ke Saudiyya

- Daga baya dai ya yi bayanin cewa ya Musulunta kuma mutane da yawa sun yi fatan tabbatarshi a addinin Musulunci

Allah na shirya wanda ya so, a lokacin da ya so. Ikon Allah ya sha gaban tunanin mutane. Allah ya haliccemu kuma ya fi mu sanin dalilin yin komai. Ya san alheri ko akasin hakan garemu.

Wannan labarin jakadan kasar Birtaniya ne dake kasar Saudiyya da ya amshi kalmar shahada ya Musulunta.

Jakadan Birtaniya, KSA Simon Collins ya koma Musulunci kuma ya yi aikin hajjinshi na farko a Makka. Labarin Musuluntarshi ya bazu ne bayan da aka dinga wallafa hotunanshi a shafin Twitter. An nuna hotonshi da matarshi sun sanya harami a gaban ofishin jakadancin Birtaniya dake birnin Makka.

Tun a lokacin an kasa ganewa; ya Musulunta ne ko a’a. Daga baya ne ya tabbatar da zargin da ake mishi inda ya wallafa gajeren rubutu a shafinshi na Twitter kamar haka: “Allah ya albarkaceku, a takaice dai na koma addinin Musulunci bayan da nayi shekaru 30 a cikin Musulmai kafin in auri matata Huda.”

KU KARANTA: Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS

Jakadan Birtaniyan ya samu sakonnin taya murna daga Musulmai dake fadin duniya. An kara mishi da fatan Allah ya tabbbatar da duga-duganshi a addinin tare da nasara.

Collins dama kwararre ne a yaren larabci kuma ya koma addinin Musulunci ne tun a shekarar 2011 kafin ya auri matarshi ‘yar asalin kasar Syria. Manyan kasar Saudiyya ne suka san ya koma addinin Musulunci a wancan lokacin.

Bayan da Collins ya karbi sakonni tare da addu’o’in mutane, ya ki yarda a tattauna dashi a kan imaninshi.

Simon Collins ne jakadan Birtaniya na farko da ya fara aikin hajji duk da akwai wasu jakadun da suka koma Musulunci kafinshi.

Ya yi jakadanci a kasashe kamar irin su Iraq, Jordan da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel