Seyi Makide ya ruguza ‘Sarakunan’ da Gwamnatin Ajimobi ta karawa matsayi

Seyi Makide ya ruguza ‘Sarakunan’ da Gwamnatin Ajimobi ta karawa matsayi

An kawo karshen rigimar Olubadan na kasar Ibadan watau Saliu Adetunji, da mutanensa. An cin ma wannan mataki ne bayan da gwamnatin jihar ta janye karin nadin da aka yi wa Sarakunan.

Tunbuke karin girmar da aka yi wa Sarakunan ya na cikin sharudan da aka gindaya domin a janye karar da ke gaban kotu. Idan ba ku manta ba shekaru biyu kenan ana rikici a masarautar.

Daga cikin wadanda su ka samu matsala da Mai martaba Olubadan na kasar Ibadan, Saliu Adetunji, akwai Otun na Olubadan, Lekan Balogun, da Balogun na Ibadan, Owolabi Olakulehin.

Lekan Balogun da Takwaransa Owolabi Olakulehin, da ke cikin majalisar Mai martaba Olubadan su na ta rikici ne bayan da tsohon gwamna ya karawa wasu masu mulkin gargajiya matsayi.

Gwamnatin Abiola Ajimobi ta daga darajar wasu Lawalai 21 zuwa matsayin Sarakuna masu cikakken iko a jihar Oyo. Abiola Ajimobi ya dauki wannan mataki da ya jawo sa-in-sa ne a 2017.

KU KARANTA: Gwamna Makinde ya bayyana abin da ya karba a matsayin albashinsa

Manyan jihar Oyo har da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo sun yi kokarin kashe wutar rikicin amma abin bai yiwu ba. Sai yanzu ne sabon gwamnatin jihar Oyo ta fara raba gardamar.

Seyi Makinde wanda ya gaji gwamnatin APC ya karbe sandunan sarautar wadannan Sarakuna da nadinsu ya jawo sabani. Yanzu za a warware rikicin na Olubadan da Sarakunan a wajen kotu.

A Watan Agustan nan, babban kotun daukaka kara ta dawo da shari’ar nadin sarauta zuwa karamin kotu. Babban kotun ta nemi masu karar su nemi hukunci a wajen Alkalin kotun tarayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel