Kasar Denmark za ta samawa dubban ‘Yan Najeriya aikin yi a kamfanin Madara

Kasar Denmark za ta samawa dubban ‘Yan Najeriya aikin yi a kamfanin Madara

Jakadan kasar Denmark a Najeriya, Jesper Kamp, ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa za ta maida hankali a kan samawa ‘Yan Najeriya aikin yi a maimakon ba ‘yan kasar gudumuwar kudi.

Ambasada Jesper Kamp ta bayyanawa Manema labarai wannan ne a wajen wani taro da aka shirya a Legas. An shirya wannan taron hadin-kai tsakanin FOSS da PAGI ne a Ranar Talata.

Wani babban jami’in kamfanin FOSS, Michael Moller, ya bayyanawa NAN cewa FOSS ta hada-kai da PAGI na Najeriya ne domin kawo dabarun da za su sa a gamsar da kasar da isasshen abinci.

Kamp ya ke cewa: “Mu na tunanin maida hankalinmu kan bunkasa kasuwanci a madadin tallafin kudi, dalilin haka shi ne mu na amfani da gudumuwar kudin domin karfafa ayyuka a Najeriya.”

KU KARANTA: Minista ta amsa tambayoyi a Majalisa game da karin VAT

An shirya taron hadin-gwiwar kungiyar FOSS ta Turai da kuma kamfanin Najeriyar ne a Ranar 19 ga Watan Nuwamban 2019, wanda Jakadan kasar Denmark din ya samu halarta da kansa.

“Nan gaba kadan, Kamfanin kasar Denmark na Arla Foods Global Nigeria, zai samawa kusan mutum 25, 000 a Najeriya hanyar samun abin yi a aikin kamfanin da ake yi a Garin Kaduna.”

Jakadan ya kara da cewa: “Fa’idar wannan aiki shi ne a samawa Najeriya isasshen nono domin kashe kishinsu na madara. Kasar Denmark ta na kan gaba wajen samar da abinci a Duniya.”

Tun 2016, kasar Denmark ta ke shirya taron nan na ‘World Food Summit’ na abinci. Jakadan ya ke cewa fa’idar taron shi ne samar da isasshen nagartattan abinci mai lafiya a fadin Duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng