Abin kunya: Bidiyon matar gwamnan Nasarawa ya bazu a duniya bayan ta kasa magana da turanci

Abin kunya: Bidiyon matar gwamnan Nasarawa ya bazu a duniya bayan ta kasa magana da turanci

- Wani bidiyo na matar gwamnan jihar Nasarawa tana kokarin hada kalmomi a rubutaccen jawabinta ya fantsama kafafen sada zumunta

- A bidiyon an ji tare da ganin uwargidan gwamnan jihar Nasarawa ta kasa furta wasu kalmomi da ke kunshe a jawabin nata

- Idan zamu tuna, watanni biyu bayan hawan gwamnan karagar mulki, ya auro sabuwar amarya Hajiya Farida daga jihar Katsina

Wani bidiyon matar gwamnan jihar Nasarawa ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta na zamani.

A bidiyon, Hajiya Silifa, uwargidan gwamnan jihar Nasarawa na ta kokarin karanta jawabinta ga mutane amma abin ya ci tura. Uwargidan gwamnan jihar Nasarawan ta je bude taron shirin MMC ne a jihar wanda gwamnan ke jagoranta.

A bidiyon, Hajiya Silifa ta kasa furta wasu kalmomi ne da ke rubuce a jawabin nata. Da abun ya kai ya kawo, Hajiya Silifa ta mika takardun da ke kunshe da kalmomin da ta kasa karantawar.

Lamarin kuwa ya jawo maganganu daga mutane masu yawa.

Idan zamu tuna, Gwamnan jihar Nasarawa ya kara aure watanni biyu bayan hayewarshi karagar mulkin jihar. Lamarin da ya jawo cece-kuce tare da rade-radin ya auro wacce zai dinga fita tarukan fitar kunya da ita.

Amma tuni gwamnan ya fito ya karyata lamarin. Ya bayyana Hajiya Silifa a matsayin uwargidanshi kuma ‘First Lady’ a jihar Nasarawa ba amaryarshi Hajiya Farida ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel