Bidiyon yadda Sadiya Haruna da Isah A Isah suke kokarin sumbatar junansu

Bidiyon yadda Sadiya Haruna da Isah A Isah suke kokarin sumbatar junansu

- Wani bidiyon jaruma Sadiya Haruna da Isah I. Isah ya jawo maganganun ma’abota kafafen sada zumunta

- A bidiyon, tsananin shaukin soyayya da suke yi a wancan lokacin ya sa Sadiya Haruna da Isa A Isa suka yi kokarin sumbatar junan su

- Daga bisani kuwa an nuno jarumin yana rokar Sadiya Haruna akan ta taimaka ta aure shi

Wani bidiyo da tashar YouTube ta Tsakar Gida ta wallafa, ya bayyana yadda Sadiya Haruna da jarumi kuma furodusa Isah I.Isah suka sake jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon an nuno jarumin da masoyiyar ta shi cikin yanayi na shauki na soyayya. A farkon bidiyon an nuno furodusan ya durkusa yana rokon jarumar ko zata tallafa mishi ta aureshi. Hakan ta faru ne a ofishinta kamar yadda furodusan ya fada, inda ita jarumar ke zaune a kan kujera.

Sannan duk a cikin bidiyon an sake nuno jarumin da ita Sadiya Haruna suna kokarin sumbatar juna yayin da wani yake daukar bidiyon su a waya.

Daga bisani kuma sai ga furodusa Isah tare da jaruma Sadiya Haruna suna bin wata waka mai suna ‘Gudun Barewa’. Ba bin wakar bane ya jawo cece-kuce ba, sutarar jikin jarumar ce da ke bayyana surar jikinta karara. Rigar da ke jikin jarumar kuwa hannun karamar rigar mata ta Vest gareta.

KU KARANTA: Kano: Budurwa ta yi yunkurin rungumar taransufoma bayan anyi mata auren dole da dan shekara 70

Idan zamu tuna, Isah I.Isah da jaruma Sadiya Haruna a kwanakin baya sun yi kaca-kaca. Lamarin da ya ja masoyan zuwa gaban kotu.

Jaruma Sadiya Haruna ta yi bidiyo inda ta bayyana cewa sun yi auren mutu’a da furodusan. A bangaren furodusan kuwa, ya fito tare da bayyana cewa jarumar matarshi ce, Abinda ya jawo maganganu kala-kala ga mabiyansu.

Bayan hargitsin da ya hada furodusan da jarumar, sun fito kafafen sada zumunta suna tonawa juna asiri. Sadiya ta zargi cewa, tsohon masoyin nata dan luwadi ne. Babu jimawa kuwa ya maka ta a kotu don zarginta da yake da bata mishi suna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel