Kwana dubu na barawo: Dubun masu garkuwa da mutane ta cika a jahar Adamawa

Kwana dubu na barawo: Dubun masu garkuwa da mutane ta cika a jahar Adamawa

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Adamawa ta samu nasarar kama wasu miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka dade suna addabar al’ummar jahar, musamman a garin Yola.

Rahoton jaridar Premium Times ta bayyana cewa wadannan miyagu sune suka sace wani hamshakin dan kasuwa a garin Yola, Alhaji Abubakar Bashar, tare da yin garkuwa da shi, basu sake shi ba har sai da aka biya miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.

KU KARANTA: Kwararowar hamada: Gwamna ya sanya kyautar naira dubu 100 ga duk mutumin daya dasa bishiya

Da yake gabatar da miyagun a gaban Yansanda, kaakakin rundunar Yansandan jahar, Sulaiman Nguroje ya bayyana cewa sun samu nasarar kamasu ne bayan samun bayanan sirri daga wasu jama’a, sa’annan ya kara da cewa a yanzu suna kokarin kamo sauran abokan aikinsu.

“Barayin biyu na da hannu cikin aikata manya manyan laifuka a garin Yola da kewaye. Mun kama daya daga cikinsu ne a Ngurore, yayin da guda kuma muka kamashi a Yola, muna cigaba da fadada samamenmu domin tabbatar da mun kama sauran miyagun.” Inji shi.

Daga cikin miyagun akwai wani mai suna Bello Abdullahi, wanda ya tabbatar ma manema labaru cewa sun hada baki ne da bafulatanin dake yi ma Alhaji Abubakar Bashar kiwon shanunsa wajen samun bayanai da suka taimaka musu wajen sace shi.

“Gaunakonsa ne ya bayyana mana lokacin da Alhaji zai je gonar a wannan rana, don haka muka yi kwantan bauna, yana isa muka kama shi, sa’annan muka nemi kudin fansa naira miliyan 20, kuma an biya. Na samu N400,000 daga cikin kudin, na yi nadamar abin da na aikata.” Inji shi.

A wani labari kuma, Rundunar Yansandan jahar Imo ta sanar da kama wata mata mai suna Ukamaka Ezike wanda ake zarginta da kashe ‘ya’yanata mata guda biyu masu kananan shekaru.

Mijin matar, kuma mahaifin yaran, mai suna Christian Ezike mazaunin unguwar Awo Idemili dake cikin karamar hukumar Orsu na jahar Imo ne ya kai kara ga Yansanda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel