Bayyanar Maryam Yahaya a harkar fim ne ya budewa kananan yara kofar shiga harkar - Tashar Tsakar Gida

Bayyanar Maryam Yahaya a harkar fim ne ya budewa kananan yara kofar shiga harkar - Tashar Tsakar Gida

- Bayyanar jaruma Maryam Yahaya a masana’antar Kannywood tun shekaru uku da suka gabata, ta bude wa kananan yara kofar shigowa masana’antar

- Hakan kuwa ya zama babban kalubale ga masana’antar don kuwa kananan ‘yan matan na amfani da sunan masana’antar don cimma wasu manufofi

- Hakan na daga cikin dalilan da suka sa hukumar tace fina-finai ta Kannywood ta hanzarta yi wa jaruman masana’antar rijista

Bayyanar Maryam Yahaya, ta bude kofar shigowar kananan ‘yan mata Kannywood.

Kusan za a iya cewa, babu wani lokaci da aka samu bunkasar kwararowar kananan yara cikin harkar fim kamar yanzu, inda abun ya zamo wani kalubale ga masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Shekaru uku da suka shude, jarumar mai karancin shekaru ta bayyana a masana’antar duk da karancin shekarunta. Ta sha banban da jaruman da ke shigowa masana’antar wadanda zaka ji sun taba aure ko kuma suna da yara da yawa.

Nasarar da sabuwar jarumar a wancan lokacin ta samu a fim din Mansoor, ya zamo kashin bayan fitowar kananan ‘yan mata don su yi fim.

Tasirin jarumar ya karu ne lokacin da ta fito a cikin fim din mijin yarinya, wanda haka ya yi wa yara da dama tasiri tare da basu karfin guiwar shigowa harkar fim. Tsananin matsin rayuwa da ake ciki shima ya taka rawar gani, saboda wasu iyayen da kansu suka dinga kwaso yaransu suna kaiwa masana’antar.

KU KARANTA: Harkar fim ce ta sani nake yin shigar mutunci a gari - Fati Shu'uma

Ganin karamar yarinya kamar Maryam Yahaya, tazo ta daukaka, tayi suna, tana hawa mota mai tsada, tana sanya suturar kece raini tare da rike waya mai tsada ya kara tada hankalin yara.

Babu wani dogon nazari a kan shin da gaske ne fim ke bata wadannan manyan kudi ko kuma wani kasuwanci take yi? Ko kuma akwai wata hanya ta karkashin kasa da take kawo mata wadannan kudaden?

Sai dai, mutane sun fi karkata a kan cewa, tana samun kudaden ne daga tarin alhairan da masoyanta ke mata daga sassa daban-daban a duniya.

Sai dai, hakan kuma ya zamo babban kalubale ga masana’antar ta fannin kasuwanci. Saboda haka, ba a kara samun wata yarinyar da ta samu daukaka kamar ta ba.

Da yake sana’ar na da wani sirri, sai ya zamana yaran da suka shigo kuma basu da aikin yi sai su yi ta yawo a gari amma ana musu kallon ‘yan fim. ‘Yan matan kan mallaki manyan motoci duk da ba wai harkar fim din ke kawo musu ba.

Hakan kuwa ce ta sa masana’antar ta tashi tsaye don yi wa jarumai rijista ta yadda za a kakkabe bara gurbi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel