Yan bindiga sun hallaka mutane da dama a Zamfara, sun kona gidaje

Yan bindiga sun hallaka mutane da dama a Zamfara, sun kona gidaje

Rahotanni sun kawo cewa wasu 'yan bindiga sun kai wa al’umman kauyen Karaye da ke karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara hari, inda suka hallaka gomman mutane, tare da kona gidaje.

Al’umman kauyen Karaye sun bayyana cewa ba su taba ganin tashin hankali irin wannan ba.

A cewarsu 'yan bindigan sun zo ne a kan babura dauke da adduna, da bindigogi tare da yi wa kauyen kawanya sannan kuma suka kwashe sa'o'i da dama su na cin karensu ba babbaka.

Sun kuma zargin cewa jami'an tsaro ba su kawo musu agaji ba, cikin wadanda aka kashe akwai mata da kananan yara da tsofaffi.

Wani mazaunin kauyen ya ce karfe shida na yamma barayin suka kewaye garin, ya ce har zuwa hudu na asuba ba su bar garin ba.

Kakakin rundunar 'yansanda a jihar ta Zamfara DSP Muhammad Shehu ya bayyana wa majiyarmu ta BBC Hausa cewa ga dukkan alama harin na ramuwar gayya ne sakamakon wani artabu da aka yi kwanakin baya tsakanin 'yan bindiga da 'yan sintiri da ake kira 'yan sa kai a yankin.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta jaddada zaben Ishaku a matsayin gwamnan Taraba

DSP Shehu ya ce mutane 14 ne suka mutu wasu 10 kuma sun samu rauni, kafin zuwan jami'an tsaro maharan sun tsere.

A halin da ake ciki dai bayanai na cewa dubban mutane sun yi hijira zuwa garin Gummi hedikwatar karamar hukumar sanadiyyar wannan hari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel