Babban magana: An gurfanar da miji kan laifin yiwa matarsa satar kudi

Babban magana: An gurfanar da miji kan laifin yiwa matarsa satar kudi

- Wani magidanci mai suna Kazeem Adetayo ya gurfana a gaban kotun Majistare na jihar Osun da ke zama a Osogbo kan laifin satar kudi N70,000 mallakar matarsa

- Dan sanda mai kara, Sufeto Kayode Adeoye, ya yi bayanin cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 6 ga watan Oktoba, 2019 da misalin karfe 6:00 na yamma a yankin Owode da ke Osogbo

- Lauyan wanda ake zargin, Okobe Najite, ya nemi a bayar da belinsa, tare da alkawarin gabatar da wadanda za su tsaya masa abun dogaro

A ranar Juma’a, an gurfanar da wani Kazeem Adetayo a gaban kotun Majistare na jihar Osun da ke zama a Osogbo kan laifin satar kudi N70,000 mallakar matarsa, Omowumi Adewale.

An gurfanar da Kazeem mai shekara 50 kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da sata.

Dan sanda mai kara, Sufeto Kayode Adeoye, ya yi bayanin cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 6 ga watan Oktoba, 2019 da misalin karfe 6:00 na yamma a yankin Owode da ke Osogbo.

A cewarsa, wanda ake zargin ya sace kudi N70,000 mallakar Omowumi a gidanta.

An tattaro cewa laifin ya kara da sashi na 516 da 390 (9) na doka ta’addanci, Cap 34 Vol. II, na dokar jihar Osun, 2002.

Kazeem bai amsa tuhumar da ake masa ba.

Lauyan wanda ake zargin, Okobe Najite, ya nemi a bayar da belinsa, tare da alkawarin gabatar da wadanda za su tsaya masa abun dogaro.

Okobe ya kuma sanar da kotu cewa lamarin abu ne na cikin gida, inda ya kara da cewa wacce ke karar a shirye take ta sasanta a wajen kotu.

Amma Omowunmi ta karyata shirin dakatar da shari’an.

KU KARANTA KUMA: Na fi asalin ‘yan daudu kwarewa wajen iya daudu a fim – Ado Gwanja

Da yake yanke, alkalin kotun Taofiq Badmus, ya amince da ba wanda zargin beli kan N100,000 tare da wadanda zai tsaya masa mutum guda.

Ya dage shari’an zuwa ranar 20 ga watan Disamba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel