Zaben Bayelsa: Jam’iyyar PDP Jonathan ya zaba – Inji Reno Omokri
Rade-radi na yawo cewa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, jam’iyyar APC ta hada-kai ta lashe zaben jihar Bayelsa. Na-kusa da tsohon shugaban sun musanya wannan.
Reno Omokri wanda ya na cikin Na-hannun-daman tsohon shugaban kasar, ya karyata zargin da ake yi wa Mai gidansa cewa ya yi wa jam’iyyar APC aiki ne ta karkashin kasa maimakon PDP.
Omokri ya karyata wannan rade-radi ne da ke yawo a kan shafinsa na dandalin sada zumunta na Tuwita, ya maida martani ga wasu daga cikin masu jifar Gooluck Jonathan da wannan zargi.
Omokri ya fadawa wani Kwamred Dan Audi cewa Jonathan ya yi iyaka yin sa a jihar Bayelsa;
Ya kai, @comr_danaudi, tsohon shugaban kasa @GEJonathan (Jonathan) da jam’iyyar @OfficialPDPNig sun yi bakin kokarinsu. Da ace su na kan mulki, da kokarinsu a harkar ilmi ya sa ka fahimci cewa ba su yi fadin da ka ke tunani ba. Mutane su na dacewa ne da irin gwamnatinsu.
KU KARANTA: Ka na da labari game da wanda ya lashe zaben Gwamnan Bayelsa
Haka zalika Omokri ya sake warware duhun da aka shiga inda ya tabbatar da cewa ya tuntunbi tsohon Mai gidan na sa a waya, kuma ya tabbatar masa da cewa bai zabi jam’iyyar APC ba.
Omokri ya rubuta: “Ya ke @boluxxxx, yanzu na yi magana da tsohon shugaban kasa @GEJonathan, kuma ya tabbatar mani da cewa bai zabi APC ba. Jam’iyyar PDP ya zaba."
Reno Omokri wanda ya yi aiki a matsayin Mai ba Jonathan shawara a lokacin da ya ke kan mulki ya kara da cewa: "PDP (Jonathan) ya sani kuma har gobe ita zai yi wa aiki. Ki fahimci wannan."
Da ya ke ba wani Jamilu Sadiq amsa tun kafin a sanar da sakamako, Omokri bayyana cewa shekarun Jonathan 61 a Duniya kuma tsawon rayuwarsa bai san wata jam’iyya face PDP ba
A cewarsa babu abin da zai sa Goodluck Jonathan ya sauya-sheka saboda rasa zabe. Omokri ya nuna cewa duk PDP ta mulki jihar Katsina na shekaru 16, Muhammadu Buhari bai taba bin ta ba.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng