Adam A Zango ya sake jaddada fitar shi daga Kannywood, bayan yaki yarda ya fito a wani sabon fim

Adam A Zango ya sake jaddada fitar shi daga Kannywood, bayan yaki yarda ya fito a wani sabon fim

- A jiya ne sannanen jarumin fina-finan Hausa, Adam Zango ya ki amsa tayin wani furodusa a kan fitowa a fim din shi

- Jarumin ya wallafa fastar sharar fagen nuna jaruman da zasu bayyana a fim din ‘Mutu ka raba’ ya soke

- Lamarin da ya kara jaddada ficewar jarumin daga masana’antar Kannywood tun kwanakin baya

A jiya ne jarumi Adam Zango, ya ki amsa tayin fitowa a fim din wani furodusa mai suna Yusuf Magarya, lamarin da ya yi matukar daurewa mutane kai. Jarumin ya bayyana hakan ne ta hanyar saka fastar fim din a shafinsa na Instagram tare da sokeshi.

Wata al’ada da mashirya fina-finai ke amfani da ita wajen zaben jaruman da zasu taka rawa a fim dinsu shine: Kera kwarya-kwaryar fasta dauke da hotunan jaruman da zasu fito a fim dinsu. Akan yi wannan fasta ne kuwa tun kafin shirye-shirye su kankama.

Wannan fasta takan zama ba zata ko albishir ga jaruman da ake so su taka rawa a fim din, don a nan ne jarumi ke sanin zai yi fim din ko akasin hakan. Bayan fitar fastar ne ake tsunduma shirye-shirye.

Irin haka ce kuwa ta faru a jiya inda wata fasta ta bayyana dauke da jarumi Adam Zango, Maryam AB Yola, Musbahu Anfara da Sabeerah Mukhtar da sunan zasu taka rawa a fim din ‘Mutu ka Raba’.

Sai dai kash! Jarumi Adam Zango bai yi farinciki akan wannan lamarin ba. A take kuwa ya wallafa fastar a shafinshi na Instagram tare da soketa. Ya kara da rubuta, “Ai na fice tuntuni, ba a tace ni ba” wanda hakan ke nuna bai amsa tayin ba, tare da jaddada batun ficewarshi daga masana’antar Kannywood.

KU KARANTA: Tirkashi: Ko uwa ta ba ta isa ta raba ni da Zahraddeen Sani ba - Adama Muhammad

Mun samu bayanan sirri na yadda ainihin wanda ya dauki nauyin shirin ke da wata kulalliya tsakaninshi da jarumin, hakan kuwa yasa bai tuntubeshi kai tsaye ba kafin fitar fastar.

Amma daraktan shirin, Aminu S.Bono ya ara ya yafa inda ya maida martani ga wani yaron Adam Zango kamar haka, “Na san saboda kai jarumin ya yi haka. Kace an je gidan rediyo an zagi jarumin. Na sa mota ta in har aka kawo min inda aka ji ana zagin Adam Zango.”

Daga baya kuwa, daraktan ya wallafa wani bidiyo inda yake cewa ya tuntubi jarumin kuma ya shaida mishi ba don shi ya yi ba. Ya yi ne don mashiryin shirin, saboda taka ka’idar da ya yi ta wallafa hotonsa ba tare da ya tuntubeshi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel